A KABILAR BODI, IYA GIRMAN TUMBINKA IYA FARIN JININKA.
A tsarin kabilar Bodi dake kasar Ethiopia, mazaje masu katon tumbi sune wadanda mata suka fi rububi kuma suka fi so da kauna.
Girman tumbinka shine yake nuna irin farin jininka a tsakanin ‘yan matan garin.
Suna gauraya jini da madara, sannan su sha domin kara kiba da kuma kara girman tumbin nasu.
‘Yan Wannan kabila ta BODI suna zaune ne a wani dan karamin tsuburi da ake kira da Omo a kasar ta Ethiopia, kuma suna matukar alfahari da wannan al’ada tasu ta rainon tumbi.Imam Auwal Warure.