Labarai

Abinda Tinubu Zai bayar akowace jaha domin abawa talakawa

Abinda Tinubu Zai bayar akowace jaha domin abawa talakawa

Gwamnatin tarayyar Najeriya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da bai wa kowacce jihar naira biliyan biyar domin sayen kayan abinci don raba wa talakawa a jihohin a matsayin kayan rage raɗaɗi..

Gwamnan jihar Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim – kaɗan bayan kammala taron majalisar tattalin arziki da aka gudanar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

Matakin na zuwa ne

Matakin na zuwa ne mako guda bayan tashin gwauron zabi da farashin kayan abinci suka yi a ƙasar da kusan kashi fiye da 20 cikin 100 cikin shekara 18.

Lamarin da masana ke dangantawa da cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

Gwamnan na jihar Borno ya ce gwamnatin tarayya ta bai wa kowane gwamna tirela biyar na shinkafa domin rabawa a jiharsa.

Zulum

Zulum ya ce gwamnonin za su sayi buhun shinkafa 100,000 da na masara 40,000 da kuma takin zamani domin raba wa al’umominsu do taimaka musu wajen rage raɗaɗin tsadar rayuwa da suke fuskanta.

Abinda Tinubu Zai bayar akowace jaha domin abawa talakawa
Abinda Tinubu Zai bayar akowace jaha domin abawa talakawa

George Akume

Tun da farko sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya ce an bai wa jihohin ƙasar 36 tirela 100 na taki da tirela 100 ma hatsi a matsayin tallafin rage raɗaɗin.

Mista Akume ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ƙaddamar da littafin tarihin Edwin Clark.

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Danna Nan: Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button