Abu 3 da manyan Jami’an tsaron ECOWAS za su mayar da hankali akansu
Ƙungiyar ECOWAS
Taron na manyan hafsoshin kungiyar ECOWAS da za a yi a burnin Burma na kasar Ghana zai maida hankali ne a kan batun aikewa da rundunar jiran ko ta kwana zuwa Nijar.
Taron na zuwa ne bayan da shugabannin kungiyar suka umurci rundunar sojin yankin ta kasance cikin shirin ko ta kwana.
ECOWAS
A yanzu a bayane ta ke cewa ECOWAS ta kara kaimi game da barazanar amfani da karfin soja domin maida kasar Nijar kan turbar mulkin dimokuradiyya tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan daya gabata.
Manyan hafsoshin
Manyan hafsoshin tsaron kungiyar ta ECOWAS za su yi taron ne a hedikwatar rundunar sojin Ghana domin tsara dabarun da za a yi amfani da su wajan amfani da karfin soja a jamhuriyar Nijar.
Za su kuma tattauna kan yawan kayayaki da yawan sojojin da ake bukata da kuma tsarin da sojojin za su bi.
A baya Ghana da Nijeriya sun jagaronci shirin wanzar da zaman lafiya a yankin na yammcin Afrika watau ECOMOG a kasashen liberia da saliyo a shekarun 1990.
Kungiyar ta kuma shiga tsakani a wasu kasashe mambobin kungiyar inda na baya baya nan ita ce Gambiya.
Sai dai kawunan mambobin kungiyar ya rabu gida biyu game da amfani da karfin soji a jamhuriyar Nijar kuma ga dukkan alamu tarrayar Afrika ta zabi hanyar amfani da kafar diflomasiya.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tabarbarewar tsaro a Nijar.
Sojoji
Sojoji 17 aka kashe yayin da 20 suka jikkata a harin kwantar bauna da mayaka masu ikikari jihadi suka kai.
Wannan shi ne hari na bakwai da aka kai wa dakarun kasar tun bayan juyin mulki kuma shi mafi muni.
Gwamnaotocin yankin sun damu da cewa tashin hankalin zai iya bazuwa zuwa yankunansu.
Sai dai masu sharhi sun yi gargadin cewa tura sojoji zuwa Nijar , wani abu ne da kan iya haifar da yaki tsakanin kasashen yankin.
Table of Contents
Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?
Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Danna Nan: Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12
Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.
Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page