Ahmad Musa Ya taimake ɗan Film baba karkuzu da maƙuddan Kuɗaɗe
Ahmad Musa
Captin Ahmed Musa Ya Aikewa Ɗan Fim Ɗin Hausa Baba Karkuzu Tallafin Naira 500,000, Ya Kuma Sa A Nemo Katafaren Gida Na Naira Miliyan 4 Zuwa Naira Miliyan 5 Zai Saya Masa
Shahararren
Shahararren ɗan ƙwallon ƙafan Nageriya, Captin Ahmed Musa MON ya ba da umarnin a Nemo gida wanda kuɗinsa ya kai Naira Miliyan 4 zuwa Naira Miliyan 5 zai sayawa ɗan Fim ɗin Hausa, Baba Karkuzu, sannan kuma a yanzu haka ya aike masa da tallafin kuɗi Naira 500,000 domin ya yi cafane duba da halin ƙunci, matsi, gami tsananin rayuwa da ya ke ciki.
Cikin wata tattaunawa da Jaridar Hausaone ta yi da shi, Captin Ahmed Musa ya bayyana cewa “Na yi magana da Baba Karkuzu ta waya, na kuma tabbatar masa na ba shi tallafin Naira 500,000 ya yi cafane. Bayan haka kuma na shaida masa cewa na ba da umarnin a nemo masa gida na Naira Miliyan 4 zuwa Naira Miliyan 5 zan saya masa daga nan kuma mu ga tayadda zan ƙara taimaka masa”. In ji Ahmed Musa.
Baba Karkuzu
A ƴan kwanakin nan ne dai aka jiyo tsohon ɗan wasan Hausan, Baba Karkuzu ya na kokawa kan halin ƙunci da ya ke ciki, tayadda har ta kai ya makance ba ya iya gani saboda ƙuncin rayuwa, har ma wasu ke nema masa tallafi a Social Media domin a taimaka masa.
Matsalar Baba Karkuzu
“Sama da shekaru 43 Ina harkar Fim, amma yanzu sai a wayi gari babu abinda za a ci a gidana. Kuma yanzu haka na daina gani, sannan kuma gidan da na ke ciki mai shi ya saka shi a kasuwa”, Cewar ɗan Fim ɗin Hausa, Baba Karkuzu.
Albishir.
Wannan labarin ya taɓa Captin Ahmed Musa sosai ya yi jimamin halin da Baba Karkuzun ya ke ciki, domin tun ya na yaro a birnin Jos ya ke ganin wasannin Baba Karkuzun a gidan talabijin na NTA. Ganin haka ya sa Captin Ahmed Musa ya nema ya yi magana da shi ta waya ya kuma yi masa wannan albishir da wannan tallafi na gida da kuɗi.
Captin
Captin Ahmed Musa mutum ne wanda ya yi shuhura wajen taimako da jinƙan al’umma, ko da a baya-bayan nan, ya sayawa wasu matasa mutum 4 manya-manyan gidaje a Kano domin su zauna da iyalansu.
Amma mizakace dangane da wannan lamarin.
Table of Contents
Table of Contents
Danna Nan: Dalilin da yasa aka canza Maryam shetty- Ganduje
Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page