Ba mu aminta da kayan tallafi a hannun gwamnoni ba – Ƴan ƙwadago
Ƙungiyoyin ƙwadago
Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun soki matakin gwamnatin tarayya na bayar da naira biliyan 180 ga jihohi domin raba wa jama’a a matsayin rage raɗaɗin cire tallafin mai.
Haɗakar ƙungiyoyin ƙwadagon NLC da TUC ta ce a yanayin yadda al’amura ke tafiya a Najeriya, ‘yan siyasa ne za su ci gajiyar tallafin na naira biliyan biyar da za a bai wa kowacce jiha, amma ba talakawan da aka fitar da kuɗaɗen domin su ba.
A ranar Alhamis ne, gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya sanar da shirin gwamnatin na bai wa kowacce jiha naira biliyan biyar da tirelolin shinkafa 180 domin rage wa jama’a zafin cire tallafin.
Matakin ya zo ne bayan wani taron Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima a Abuja.
Gwamnan na Borno ya ce, jihohin za su yi amfani da naira biliyan biyar ɗin ne domin sayen buhunan shinkafa 100,000 da masara da kuma takin zamani, waɗanda za a raba ga talakawa.
Zulum
Zulum ya ce bisa la’akari da halin da ake ciki da kuma ƙudurin gwamnati na shawo kan tashin gwauron zabi da farashin kayan abinci ke yi ya sa gwamnatin tarayyar a makon da ya gabata ma ta bayar da tirelolin shinkafa biyar-biyar ga kowacce jiha a ƙasar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa dukkan matakai da gwamnatin ta ɓullo da su saboda janye tallafin man fetur, ba su samu karɓuwa ba wajen ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar, domin tun da farko sun ba da sharaɗin cewa gwamnati ta gyara matatun mai na cikin gida, kafin janye tallafin.
Da suke mayar da martani ga tanade-tanaden gwamnati na tallafin rage raɗaɗin, ‘yan ƙwadagon sun nuna shakku a kan yiwuwar samun nasarar shirin.
Babban sakataren ƙungiyar NLC, Mista Chris Onyeka, ya bayyana mamaki a kan yadda gwamnatin tarayya ta ba da kuɗin tallafin ga gwamnoni waɗanda ya ce da yawansu sun ƙi biyan mafi ƙarancin albashi ma a jihohinsu.
Mista Onyeka ya yi watsi da yawan kuɗin tallafin, da cewa bai taka kara ya karya ba, inda ya ƙara da cewa ba zai kai ga waɗanda ake son su amfana ba.
Ya nuna cewa shirin shi kansa wata dabara ce ta gwamnatin Najeriya ta kauce wa matsayar da suka cimma yayin tattaunawa a baya.
Babban sakataren
Babban sakataren ya ce ƙungiyarsu ta NLC za ta ci gaba da yin tsayin daka a kan matsayinta har sai an tattauna, da kuma aiwatar da su yadda ya dace.
“Idan gwamnatin tarayya tana son ta yi ƙafar-ungulu ga batun tattaunawa, sai ta ƙirƙiri matsaloli,” in ji shi.
Ya ce: “Da farko gwamnatin tarayya ta fara bayar da haɗin kai a lokacin da ta fara tattaunawa da NLC, to amma a ce yanzu sun kewaye sun ba gwamnoni kuɗi tamkar zagon-ƙasa ne ga tattaunawa, da zaman lafiya da dimokraɗiyya, saboda ya saɓa wa tsari”.
Haka shi ma mataimakin shugaban ƙungiyar TUC, Tommy Etim, ya yi suka ga shirin tallafin, inda ya ce sanarwa daban, aiwatarwa kuma daban.
Ya ba da misalin tallafin annobar korona a 2020, inda ya ce an ɓoye kayan abinci, yayin da ‘yan ƙasa ke fama da yunwa.
Haka kuma ya ƙara ba da misalin tallafin kuɗin Paris Club, inda ya ce wasu gwamnoni sun ɓoye kuɗin a bankuna, yayin da mutane ke cikin yunwa.
Mataimakin shugaban na TUC
Mataimakin shugaban na TUC ya ce, akwai buƙatar a kafa wani kwamiti ko hukuma da za ta bi diddigin rabon tallafin, matuƙar ana son shirin ya yi nasara, idan kuma ba haka ba, “abu ne mawuyaci ya kai ga waɗanda aka yi nufin bai wa.”
“Ya kamata kowa ya san cikakken bayanin abin da aka bai wa kowacce jiha da yadda za a raba,” in ji shi.
Tommy Etim
Tommy Etim ya kuma ce: “sai an samu waɗanda za su bi diddigi yadda ya kamata, domin gwamnonin su yi cikakken bayani idan ta kama kan yadda aka raba tallafin.”
Shi kuwa shugaban ƙungiyar NLC Joe Ajaero, ya yi nuni ne da yadda yake ganin gwamnatin tarayyar ba ta ɗauki rayuwar talaka da muhimmanci ba.
Ya ce, idan aka yi lissafin naira biliyan biyar sau 36 wato yawan jihohin ƙasar, za a samu naira biliyan 180, kuma idan aka raba wannan kuɗi da alƙaluman da hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta fitar na mutum miliyan 133 da ke cikin talauci, kowa zai samu naira dubu biyu ne kawai.
Shugaban ya ce wannan a hukumance kenan, wanda kuma yawan talakawan ya fi alƙaluman da aka bayar, saboda haka wannan tallafin ba wani amfani da zai yi, idan aka yi lissafi.
Haka su ma tirelolin shinkafar da za a bayar, ya ce idan aka yi lissafi da yawan talakawan za a ga wani ko kofi ɗaya na shinkafar ba zai samu ba, domin ba za ta isa ba.
”Wannan shi ne abin da ya kamata mu yi? Wannan shi ne ya dace gwamnati ta yi? Mun mutunta jama’armu a ce mun ba su kofin shinkafa da naira dubu biyu? Wannan shi ne tallafi?” In ji Ajaero.
Ya ce ya kamata gwamnati ta ɗauki mulkin jama’a da muhimmanci ta yi abin da zai amfani mutane.
Ƙungiyoyin sun shiga zanga-zanga a faɗin ƙasar ta nuna ƙin amincewarsu ga janye tallafin, wanda ake ganin ya haddasa tsadar rayuwa tare da jefa jama’a cikin mawuyacin hali na fatara da talauci.
Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan matsala da tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Table of Contents
Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki
Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.
Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page