Barcelona na son Bernado Silva 2023
Barcelona
Yayin da ɗan wasan Faransa Ousmane Dembele ke shirin komawa PSG, ƙungiyarsa ta Barcelona ta karkata hankalinta kan ɗan wasan Manchester City Bernado Silva mai shekara 28.(Mundo Deportivo – in Spanish)
Aikin kocin West Ham David Mayors na cikin haɗari saboda damuwar da ake ƙara fuskanta a ƙungiyar kan ‘yan wasan da ake son saya. (Mail)
West Ham
West Ham ta shirya tattaunawa da Ajax kan ɗan wasan Mexico Edison Alvarez, biyo bayan cimma yarjejeniyar kai da kai da ɗan wasan mai shekara 25. (Fabrizio Romano)
Manchester United
Kocin Manchester United Erik ten Hag na son ƙungiyar ta ɗauko ɗan wasan tsakiyar Real Madrid Aurelien Tchouameni, wanda ƙungiyar Bayern Munich take nema itama. (Sport – in Spanish)
Fiorentina
Fiorentina ta ajiye ɗan wasan tsakiyar Moroko Sofyan Amrabat a wasan da za ta buga a ƙarshen mako na share fagen fara ƙakar wasanni, saboda neman da Manchester United ke yi masa!. (Manchester Evening News)
Real Madrid
Real Madrid ta shirya ƙalubalantar Chelsea kan ɗaukar ɗan wasan Juventus Dusan Vlahovic mai shekara 23, idan haƙarta ba ta cimma ruwa ba kan ɗan wasan PSG da Faransa Kylian Mbappe!. (Cadenaser – in Spanish)
Chelsea
Chelsea na neman ɗan wasan Argentina na tsakiya Leandro Parades mai shekara 29 daga PSG bayan sun fusata da cinikin ɗan wasan Ecuador da Brighton Moises Caicedo mai shekara 21. (Standard)
Tottenham
Tottenham! na dab da ɗaukar ɗan wasan dan wasan Wolsburg Micky van de Ven mai shekara 22 kan kuɗi yuro miliyan 40 amma za su iya kai wa miliyan 50 daga ƙarshen cinikin. (Sky Sports)
Manchester City
Manchester City ta yi wa ɗan wasan Ingila Kyle Walker tayin stawaita kwantaragi, lokacin da Bayern Munich ke tsaka da neman ɗan wasan. (Athletic – subscription required)
Brighton
Brighton ta nuna sha’awarta kan ɗan wasan tsakiyar Inter Milan Kristjan Asllani, mai shekara 21. (Tuttomercatoweb.com – in Italian)
Inter Milan
Inter Milan ta daidaita da golan Bayern Munich Yann Sommer mai shekara 34, kuma za a duba lafiyarsa nan d mako mai zuwa, ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyu a Inter, bayan ƙarewar kwantaraginsa a Bayern. (Football Italia)
Atlanta
Atlanta ta shirya ɗaukaukar ɗan wasan West Ham ɗan kasar Italiya Gianluca Scamacce mai shekara 24. (Football Italia)
Barcelona a shirye take ta karɓi fan miliyan 8.6 kan ɗan wasanta ɗan ƙasar Amurka Sergino Dest. (Athletic – subscription required)
Man Utd ta yi nasara kan Lens a wasan sada zumunta
Marcus Rashford ya taka rawar gani yayin da Manchester United yin nasara da ci 3-1 a wsana sada zumunta da Manchester United ta buga da kungiyar Lens a Old Trafford.
Duk da cewa Lens ta fara zura kwallo a raga bayan Andre Onana ya yi sake kwallo ta wuce shi daga tsakiyan fili, Rashford ya farke kafin Anthony ya jefa wa United kawllo na biyu.
An gabatar da sabon dan wasa Rasmus Hojlund ga ‘yan kallo 57,802 kafin a fara wasan amma Rashford ya nuna cewa United na da dan wasan gaba mai hazaka, inda ya yi sanadin bugun kwallon Casemiro ya karkatar cikin raga don tabbatar da nasaran tawagar Eric Ten Hag.
A ranar Lahadi ne kungiyar za ta kammala atisayen tunkarar kakar wasa ta bana da Athletic Bilbao a birnin Dublin.
Danna Nan: Gasar kofin Duniya: Morocco ta cire colombia, Rauni zai hana Jesus fara gasar Firimiya
Danna Nan: Gasar kofin Duniya: Morocco ta cire colombia, Rauni zai hana Jesus fara gasar Firimiya
Table of Contents
Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.
Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page