Labarai

Bayern na tattaunawa da Tottenham kan Kane, Fabinho ya koma Al-Ittihad

Bayern na tattaunawa da Tottenham kan Kane, Fabinho ya koma Al-Ittihad

Ɗan wasan Brazil Fabinho ya kammala koma wa ƙungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya daga Liverpool a kan kwantiragin shekara uku.

Dan wasan mai shekara 29, bai tafi tare da tawagar ‘yan wasan Liverpool zuwa sansanin horo na baya-bayan nan a ƙasar Jamus ba, bayan tayin da Al-Ittihad ta yi masa na fam miliyan 40.

Haka kuma Fabinho ya fice daga tafiyar da ƙungiyar ke yi a ƙasar Singapore yayin da aka kammala gudanar da cinikin.

Fabinho shi ne babban ɗan wasa na baya-bayan nan da Al-Ittihad ta ɗauka cikin ‘yan wasan da ke kwarara zuwa Gasar Saudi Pro League.

Fabinho ‘zai buga karawa da Manchester City’1 Fabrairu 2021

Tafiyar Fabinho Saudiyya na neman rugujewa saboda karnuka, Tottenham da Kane saura ƙiris24 Yuli 2023

Al-Hilal na son Neymar da Mourinho, Arsenal za ta sayi Castagne12 Yuni 2023

Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or, kuma tsohon ɗan wasan Real Madrid Karim Benzema da tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea N’Golo Kante da tsohon dan wasan Celtic Jota duk sun koma ƙungiyar da tsohon kocin Spurs da Wolves Nuno Espirito Santo ke horaswa.

Al-Ittihad ta ce ta ɗauko Fabinho ne a ƙoƙarinta na ƙarfafa ayarin kulob ɗin da fitattun ‘yan wasa, waɗanda za su taimaka wajen inganta ƙungiyar, su kuma ba ta damar lashe gasanni a cikin gida da kuma ƙetare.

BAYERN NA TATTAUNAWA DA TOTTENHAM KAN KANE

Bayern Munich ta shirya biyan kuɗin da ba ta taɓa kashewa a kan wani ɗan wasa don ɗaukar Harry Kane daga Tottenham Hotspur.

Shugabannin ƙungiyar za su tashi zuwa Landan domin ganawa da shugaban Tottenham Daniel Levy inda za su yi musayar ra’ayi game da ciniki ɗan wasan.

Kuɗi mafi yawa da Bayern ta taɓa kashewa wajen sayen wani ɗan wasa shi ne Yuro Miliyan 80 da suka bai wa Athletico Madrid a kan Lucas Hernandez a 2019.

Sun shirya biyan fiye da haka a kan Kane duk da yake ya rage saura wata 12 a kwantiraginsa.

Kane ya zama na biyu a yawan cin kwallaye a Premier League6 Mayu 2023

Man Utd ta kawo karshen zawarcin Kane, Chelsea za ta yi gogayya da Arsenal a kan Caicedo15 Yuni 2023

Real Madrid za ta ɗauki Kane madadin Benzema5 Yuni 2023

A makon jiya ne, ƙungiyoyin ya kamata a ce sun gana, amma sai aka ɗage zaman, yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu game da makomar kyaftin ɗin na Ingila, Kane.

PSG NA ZAWARCIN DEMBELE

Akwai alamun cewa Ousmane Dembele zai iya barin Barcelona a wannan bazara, inda aka samu rahoton cewa Paris St-Germain na sha’awar sayen ɗan wasan.

Fabrizio Romano ya ruwaito cewa tuni Bafaranshen ya amince da yarjejeniyar shekara biyar da zakarun Gasar Ligue 1 .

Ɗan wasan mai shekara 26 yana da kuɗin tafiya na Yuro miliyan 50 (£43m) a kwantiraginsa da Barca – wanda ya ƙare a ranar 1 ga watan Agusta. Babu tabbas a kan ko PSG ta miƙa tayi a cikin wannan wa’adin.

An kuma samu labarin cewa kocin Barca, Xavi ya shiga tsakani domin ya shawo kan Dembele ya ci gaba da zama a kulob ɗin.

Barca ta ja kunnen Dembele ko kuma ta sayar da shi20 Janairu 2022

Barcelona ta kara kwantiragin kaka biyu ga Dembele14 Yuli 2022

Liverpool ta tuntuɓi Dembele, Torres zai koma United30 Mayu 2022

Yanzu za a fara tattaunawa.

Barcelona ta ba shi kwana biyar ya zo da tayi daga PSG.

A halin yanzu, Barcelona ba ta karɓi tayi daga PSG a kan ɗan wasan ba.

Danna Nan: PSG za ta sayi Ousmane Dembele daga Barcelona, Bayern Munich na son David Raya

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button