Labarai

Dalilin da yasa aka canza Maryam shetty~Ganduje

Dalilin da yasa aka canza Maryam shetty~Ganduje

Abdullahi Ganduje ya zama shugaban APC a watan Yuli bayan ya yi gwamnan Kano tsawon shekara takwas

Dalilin

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce wasu ‘yan ba-ni-na-iya ne suka bayar da sunan Maryam Shetty don naɗa ta minista daga Kano ba tare da saninsa ba.

Sai dai, ya ce shugaban ƙasa yana da damar naɗa mutanen da yake son tafiya da su a muƙaman ministoci daga jihohin ƙasar bisa la’akari da tsare-tsarensa da ƙwarewar mutanen da kuma sauran buƙatu.

A wata hira da ya yi da wasu kafofin yaɗa labarai ranar Asabar, tsohon gwamnan, wanda shi ne jagoran jam’iyyar a Kano, ya ce ba shi da cikakkiyar masaniya a kan Maryam Shetty, hasali ma ba su santa ba a matsayinsu na jagororin APC daga Kano.

maryam shetty

“Don haka ka ga ba mu da wani ma’auni da za mu ce za ta iya ko ba za ta iya wannan aiki ba idan aka nemi shawararmu,” a cewarsa.

Ganduje ya ce martanin da mutane suka yi ta bayyanawa a shafukan sada zumunta, shi ma ya taka rawa wajen ɗaukar matakin sauya sunan Dakta Maryam Shetty, bayan wasu sun riƙa nuna cewa ba za ta iya riƙe muƙamin minista a Najeriya ba kasancewar ba ta taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba.

shugaba

Shugaban na APC ya ce da haka ne labari ya je har wajen shugaban ƙasa, wanda ya kira Ganduje don jin shawararsa.

”Ya ce min ga fa abin da ke faruwa, shin kai ka bayar da sunanta? Sai na ce masa a’a sam sam, ba ni ba ne, ban ma sani ba, daga nan ya ce to ya ka gani? akwai buƙatar a canja?, sai na ce masa ƙwarai da gaske kuwa”, in ji tsohon gwamnan na Kano.

Ganduje

Ganduje ya ce muƙamin minista, matsayi ne da ke buƙatar dattaku da sani (ƙwarewa), sannan yana buƙatar taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnati a siyasance.

”To idan ka auna waɗannan abubuwa kuwa, ai mu ya kamata a tambaya, in dai ana so a bayar da wakilci daga jihar Kano”, in ji shi.

Ya ce ko da wani can ya bayar da wata shawara, to ya kamata a tuntuɓe su , idan ya dace sai su ba da goyon baya.

Dalilin da yasa aka canza Maryam shetty- Ganduje
Dalilin da yasa aka canza Maryam shetty- Ganduje

Cire sunan Maryam Shetty daga jerin ministocin Shugaba Tinubu, kamar bayyana sunanta a cikin waɗanda za a naɗa tun farko, ya yi matuƙar janyo muhawara musamman a tsakanin matasa da matan ƙasar.

Da yawa suna cewa abin da aka yi ya nuna rashin dacewa da kuma hangen nesa.

Table of Contents

Amma mizakace dangane da wannan lamarin.

Danna Nan: Hamisu Breaker Ke ɗaya official music 2023

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button