Labarai

Ecowas na shirin tura dakarunta domin kai yaƙi Nijar

Ecowas na shirin tura dakarunta domin kai yaƙi Nijar

Ecowas ta umarci dakarunta su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar

Acikin shirin namu nayau zakuji cewa, shugabani ƙasashen Ecowas sun ba da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.

Ecowas na shirin tura dakarunta domin kai yaƙi Nijar
Ecowas na shirin tura dakarunta domin kai yaƙi Nijar

Sanarwar

Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin bijiro da dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta wa Nijar aiki da ƙudurorin ƙungiyar ƙasashen.

Abuja

Sun cimma wannan matsaya ce yayin taron gaggawa da suka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Cikin sauƙi, ba za a iya fayyacewa ƙarara, a kan ko umarnin yana nufin dakarun sojin Ecowas za su auka wa Nijar da yaƙi, ko kuma za su ɗaura ɗamara su zauna cikin shirin yaƙi ba ne kawai.

Tun da farko, Ecowas ta bai sojojin da suka yi juyin mulki wa’adin kwana bakwai don su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed da suka hamɓarar daga mulki, ko su fuskanci matakin amfani da ƙarfin soji.

Shugabannin

Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da suka aika da kuma muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron Ecowas suka bayar da kuma sauran bayanan da hukumar ƙungiyar ƙasashen ta gabatar.

Sun kuma nanata Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.

Ƙungiyar ta ce za ta tabbatar da ganin ana aiki da duk ƙudurorinta kuma har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke.

Shugabannin sun kuma ɗora wa jagororin Ecowas alhakin ci gaba da bibiyar takunkuman da aka ƙaƙaba wa shugabannin juyin mulki a Nijar

Haka zalika, sun gargaɗi waɗanda suka ce suna kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Nijar su guji yin haka.

Amma mizakace dangane da wannan lamarin.

Danna Nan:Ahmad Musa Ya taimake ɗan Film baba karkuzu da maƙuddan Kuɗaɗe

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button