Ecowas tace bata amince da sojiji suyi shekara 3 a mulkin Nijar ba
Ecowas
Kungiyar Ecowas ta ce ba za ta amince da maganar da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi ba, cewa zai mayar da ƙasar kan tafarkin dimokraɗiyayya cikin shekara uku masu zuwa.
Janar Abdourahmane Tchian
Cikin wata sanarwa da shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahmane Tchiani ya fitar da maraicen ranar Asabar ya ce zai miƙa mulki hannun farar hula cikin shekara uku.
Tattaunawa da Hausaone
A tattaunawarsa da manema labarai, kwamishinan harkokin siyasa da tsaro da tabbatar zaman lafiya na Ecowas, Abdel-Fatau Musa, ya ce yana ganin sanarwar da Janar Tchiani ya fitar dabara ce ta buƙatar tattaunawa.
Ya ƙara da cewa ya kamata a ce jagororin sojin Nijar sun mayar da hankali wajen yaƙar ‘yan ta’adda, maimakon harkokin mulkin ƙasar.
Ƙungiyar dai na buƙatar sojojin su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar kan mulki ba tare da ɓata lokaci ba.
Ecowas ta kuma yi barazanar amfani da ƙarfin soji domin mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Sanarwa
To sai dai cikin sanarwar da ya fitar, ranar Asabar, Janar Tchiani ya yi gargaɗin cewar amfani da ƙarfin soji ka iya wargaza zaman lafiyar ilahirin yankin yammacin Afirka.
Table of Contents
Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?
Idan Kanada labarin da akeso a wallafa acikin wannan shafin namu mai albarka,zaka iya yimuna comments ta wajenda munka tanadarmuku.
Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki
Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.
Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page
Hausaone tashar muce akoda yaushe