Ecowas tace batada ƙudurin ruguza Nijar
Ecowas
Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (Ecowas) ta yi watsi da zarge-zargen cewa wasu ne daga ƙasashen waje ke ingiza ta a kan lallai sai tilasta wa sojojin Nijar, mayar da ƙasar kan tafarkin tsarin mulki.
“Ecowas, ƙungiyar ƙasashe ce mai aiki da dokoki da tsare-tsare, ƙa’idoji da ladubban da suka kafa ta.
Muradin Ecowas
Muradinmu shi ne mu kare haƙƙoƙin al’ummarmu,” Omar Touray, shugaban hukumar Ecowas ya ce a lokacin wani jawabi da ya gabatar a Abuja, babban birnin Najeriya.
Omar Touray
Omar Touray ya ƙara da cewa Ecowas ba ta ƙaddamar da yaƙi a kan al’ummar Nijar ba, yayin da ake fuskantar barazana kan yiwuwar amfani da ƙrfin soji da nufin mayar da shugaban ƙasar wanda aka zaɓa a kan tafarkin dimokraɗiyya.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar ba ta da niyyar mayar da Nijar, ƙasar da za a ruguza. “Ecowas ba za ta taɓa barin al’ummar Nijar su sha wahala a hannun maƙiya a cikin gida da kuma ƙetare ba.
Kawai dai Ecowas ta damu ne da abin da zai kyautata rayuwar al’ummar Nijar.”
Omar Touray ya ce Ecowas za ta yi amfani da “duk wata dama da take da ita” don mayar da zaman doka a ƙasar.
Table of Contents
Ya ƙara da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a watan Yuli tun farko “sun bijire wa duk wani ƙoƙarinmu na diflomasiyya” kuma ya ce “ba za a taɓa amincewa da” mulkin riƙon ƙwarya tsawon shekara uku da sojojin juyin mulkin suka sanar ba.
Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan matsala da tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Danna Nan: Godwin Emefiele na neman sassaucin kotu
Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka, Sannan kutura wannan labarin zuwa ga ƴan uwa da abokanin arziki domin suma sugani.
Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page