Labarai

Farashin man fetur ya doshi naira 800 a jihohin Najeriya

Farashin man fetur ya doshi naira 800 a jihohin Najeriya

Bayanai daga Najeriya na cewa farashin litar man fetur ya kai naira 650 a jihohin Borno Oyo da kuma Delta.

Karin da ke zuwa dai-dai lokacin da dillalan mai a kasar suka sanar da cewa nan ba da jimawa ba za’a fara sayar da a tsakanin naira 680 zuwa naira 720, ikirarin da kamfanin NNPC ya musanta.

Har yanzu dai ‘yan kasar na ci gaba da zubawa kungiyoyin kwadago idanu don ganin irin matakin da  zasu dauka kan tashin farashin kayayyaki, da kuma yadda gwamnatin kasar ke nuna halin ko in kula game da mayuwacin halin da ‘yan Najeriyar ke ciki.

A farkon makon da ya kare ne dilallan man fetur din suka ce akwai alamun da ke nuna cewa farashin mai musamman a arewacin kasar zai tasamman naira 800, saboda tsadar kudin dakon man da suke biya.

A cewar su, a yanzu suna biyan akalla naira 34 koma fiye da haka a matsayin kudin dakon man fetur kan kowacce lita.

Wannan bayani na dilallan man fetur din tuni ya fara jefa razani a zukatan yan kasar, sai dai sun dan sami sauki da jin cewa hakan ba zata yiwu ba daga kamfanin man fetur na NNPC.

To sai dai da alama batun na dilallan man fetur din ya fara tabbata, la’akari da yadda aka wayi gari da ganin karin na dare daya a wasu jihohin.

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Farashin man fetur ya doshi naira 800 a jihohin Najeriya
Farashin man fetur ya doshi naira 800 a jihohin Najeriya

Danna Nan: Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button