Labarai

Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Farashin abinci a duniya

Farashin abinci a duniya kamar su shinkafa da man kayan gwari zai yi tashin da bai tabayi ba cikin shekara 12.

Hukumar Abinci

Wannan na cikin wani rahoto da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fiyar a wannan watan na Agusta, wanda ta ce hakan ya biyo bayan ficewar Rasha ne daga yarjejeniyar fitar da abinci da aka cimma tsakaninta da Ukraine ta ruwa.

FAO ta ce alƙalumanta sun nuna an samu ƙaruwar kashi 12.1 na farashin Man girki bayan irin wannan tashin da aka samu cikin watanni bakwai a jere.

Farashin shinkafa

Farashin shinkafa ma ya tashi da kashi 1.3 a watan Yuli idan aka kwatanta da watan Yuni, kamar yadda FAO ta bayyana a ranar Juma’a.

faɗuwar kayayyakin abinci

An riƙa samun faɗuwar kayayyakin abinci a duniya a bara wayan wani tashin gwauron zabi da abincin ya yi lokacin da ake tsaka da rikicin Rasha.

Ƙara samun katsewar fitar da abinci daga da aka samu a bayan nan bayan ficewar Rasha daga cikin yarjejeniyar fitar da abinci da aka cimma da Ukraine, ya sanya ƙayan abinci tashi a faɗin duniya.

Rasha da Ukraine

Ƙasashen Rasha da Ukraine ne ke kan gaba wajen noma tare da fitar da alƙama da wasu sauran nau’o’in hatsi da akan iya sarrafawa a fitar da su duniya, musamman zuwa nahiyar Afrika da Gabas ta tsakiya da kuma Asiya inda miliyoyin mutane ke fama yunwa.

“Ƙasashen da suka dogara da shigo da abinci za su yi matuƙar kaɗuwa ta tashin farashin, saboda zai janyo hauhawar farashin sauran kayayyaki da talauci da matsalar abinci,” in ji rahoton.

Rashin amfani da Baharul Aswad wajen fitar da hatsi ya janyo tashin farashin alƙama da kashi 1.6 a watan Yuli idan aka kwatanta da wata Yuni.

Rahoton

Rahoton hukumar ya ce wani abu da zai ƙara tayar da hankalin duniya shi ne haramcin fitar da shinkafa da India ta yi, wanda ya sanya ƴan kasuwar ƙasar ɓoye wadda suke da ita a hannu zuwa kasuwannin duniya.

Haramcin fitar da shinkafa daga Indiya da kuma ficewar Rasha daga yarjejeniyarta da Ukraine ya sanya farashin shinkafa ya tashi da kashi 2.8 a watan Yuli, ya kuma ƙaru da kashi 19.7 a wannan shekarar, mafi yawa tun Satumbar 2011, in ji FAO

Wannan lamari sai ya fi shafar ƙasashen da ke yankin Kudu da Hamadar Sahara saboda su ne suka fi sayo shinkafa daga waje.

Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12
Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Danna Nan: Yanda ake sukar tinubu akan yunƙurin tura sojoji Nijar

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button