Labarai

Fati Yola – Na samu komai a rayuwa saura miji.

Fati Yola – Na samu komai a rayuwa saura miji.

Tsohuwar jaruma da ta dade ana damawa da ita a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Fatima Muhammad wacce aka fi sani da Fati Yola, ta bayyana burin da ta ke so ta cimma a nan gaba, bayan ta zama tama babbar Jaruma a cikin wadda duniya ta san ta, kuma ta ke yin alfahari da ita.

Kazalika jarumar ta bayyana bukatar ta ne, a lokacin da take tattaunawa da wakilin jaridar Dimokuradiyya, bayan ya ke yi mata tambaya a burin da ta ke so ta cimma a harkar fim, in da ta ke cewa.

Fati yola
Fati yola

“Gaskiya sai godiyar Allah, shi buri na rayuwa, ka yi addu’ar Allah ya ba ka abin da ka ke so. Don haka iya gwargwado zan iya cewa, na cimma buri na, sai dai guda daya da na ke fatan Allah ya cika mun shi ne aure. A yanzu babban buri na shi ne na yi aure. Amma duk wani abu da a ke samu, to na gode Allah, don zan samu abin da zan ci na ciyar da wani nawa har ma wanda ban sani ba, in saka suturar da raina ya ke so, kuma in hau kalar motar da na ke so, in yi rayuwa ta cikin jin dadi kamar yadda duk wani mai rufin asiri zai yi. ” a cewar ta.

Dangane da yadda a ke kallon mata ‘yan fim suna da aji wanda ba kowa za su aure ba kuwa cewa ta yi.

” To ai babu ruwan aure da aji, don za ka ga mace duk ajin ta idan ta hadu da abin da ran ta ya ke so, ko ta fi shi aji za ta iya auren sa. Don haka mace ba ta fim karfin namiji ko ta fi shi kudi, idan dai tana son sa, ka san mace, tana da alkawari ta na iya takura rayuwar ta, ta zauna da abin da take so har ta cimma burin ta. Idan ka ji mutum ya na shakkar mu to da ma can ba da gaske ya ke yi ba. Allah ya shiga tsakanin mu da shi.

Duk wanda ya ke da gaskiya zai iya neman ta ko ya bayyana abunda yakeso agaremu tawannan shafi inji ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button