Labarai

Gasar kofin Duniya: Morocco ta cire colombia, Rauni zai hana Jesus fara gasar FIRIMIYA

Gasar kofin Duniya: Morocco ta cire colombia, Rauni zai hana Jesus fara gasar Firimiya

Morocco ta cire colombia daga gasar cin Kofin Duniya ta mata

Morocco ta doke Columbia da ci daya mai ban haushi, abin da kuma ya ba ta damar tsallakwa zuwa zagayen dab da kusa da na ƙarshe a gasar cin Kofin Duniya ta mata da ke gudana a Australiya da New Zealand.

Sakamakon na nufin cewa Jamus ta kasa fitowa daga rukunin inda ta yi kunnen doki da Koriya ta kudu.

Jamus na bukatar ta ci wasanta domin ta sami damar shiga zagaye na biyu a gasar amma ta kasa cimma wannan burin.

Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin kasar Jamus da ta kasa kai wa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya..

Morocco, wadda ta sha kashi a hannun Jamus da ci 6-0 a wasan ta na farko kafin ta yi nasara a wasanni biyu a jere – za ta kara da Faransa a Adelaide a zagaye na biyu.

Colombia, wadda ta samu nasara a wasanninta biyu na farko ta kasance mai jan ragamar rukunin kuma za ta kara da Jamaica a birnin Melbourne a wasan dab da kusa da na ƙarshe ranar 8 ga watan Agusta.

Awani labari kuma zakuji cewa An yi wa dan wasan gaba na Arsenal, Gabriel Jesus karamar tiyata a gwiwarsa kuma ba zai buga wasannin farkon gasar Firimiya ta bana ba.

Jesus bai taka leda ba a wasan da suka doke Monaco a wasan sada zumunta da suka buga ranar Laraba ba kuma kocin kungiyar Mikel Arteta ya tabbatar da cewa dan wasan na Brazil zai yi jinya zuwa wasu makonni.

Raunin dan wasan mai shekaru 26 na da alaka da matsalar gwiwa da ya samu a kakar wasan da ta wuce, wanda kuma ya bukaci a yi masa tiyata.

Da yake magana bayan Arsenal ta yi nasara kan Monaco da ci 6-5 a bugun fenariti bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a filin wasa na Emirates, kocin na Gunners ya ce Jesus ya fara jin zafi a gwiwarsa a makonnin da suka gabata.

Raunin dan wasan ya zo ne kwanaki hudu kafin Arsenal ta fafata da Manchester City a gasar Community Shield da kuma kwanaki 10 kafin wasansu na farko a gasar Premier da Nottingham Forest.

Danna Nan: Lionel Messi ya ci kwallo biyu a wasan Inter Miami

Danna Nan: PSG za ta sayi Ousmane Dembele daga Barcelona, Bayern Munich na son David Raya

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin : HAUSAONE


Gasar kofin Duniya: Morocco ta cire colombia, Rauni zai hana Jesus fara gasar Firimiya

Gasar kofin Duniya: Morocco ta cire colombia, Rauni zai hana Jesus fara gasar Firimiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button