Labarai

Godwin Emefiele na neman sassaucin kotu

Godwin Emefiele na neman sassaucin kotu

Godwin Emefiele

Acikin shirin namu nayau zakuji cewa, Gwamnan bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emeifiele ya nemi samun sauki daga jerin bincike da tuhume-tuhumen da yake fuskanta kan aikata ba daidai dai ba.

Inda ya gabatar da tayin yarjejeniyar da ake kira da ‘plea bargain’ a turance, wato yarjejeniya tsakanin wanda ake kara da masu gabatar da kara.

Wanda ake karar zai amince ya amsa wasu, ko kuma dukkanin laifukan da ake tuhumar shi da aikata wa, domin samun rangwame ba tare da fuskantar dauri ko hukuncin kotu ba. 

Bayanai daga wasu majiyoyi

Bayanai daga wasu majiyoyi sun ce, a matakin na sasantawa a wajen kotu, Emefiele zai mika dukkanin kudade da kadarorin da ake  tuhumarsa da yin rub da ciki akansu.

Sai dai har yanzu babu wani karin bayani ko hujjar da ke tabbatar da alakanta  shi da wata dukiya ko kudaden haramun da ya halasta. 

Muddin bangaren masu gabatar da kara ya amince da tayín Emefiele, hakan na nufin tabbatar da kawo karshen matsayinsa na gwamnan bankin Najeriya, inda za a nada sabon shugaban babban bankin na dindindin. 

Zalika ya zama dole Emefiele da makusantansa su janye duk wata kara da suka shigar gaban kotu kan gwamnati, musamman dangane da ci gaba da tsare shi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ke yi. 

Wane fata kukeyiwa tsohon gwamnan bankin Najeriya ahalin yanzu, akan wannan Shari’a da ake cigaba da saurare ?.

Emefiele
Emefiele

Muna rokon Allah

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan matsala da tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka, Sannan kutura wannan labarin zuwa ga ƴan uwa da abokanin arziki domin suma sugani.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button