Labarai

Inter Milan na son dan gaban Arsenal Folarin Balogun 1

Inter Milan na son dan gaban Arsenal Folarin Balogun 1

Inter Milan

Inter Milan taƙagu da son dan gaban Arsenal dan kasar Amurka Folarin Balogun, mai shekara 22, bayan ta rasa dan gaban West Ham Gianluca Scamacca, wanda zai koma Atalanta. (Express)

Inter Milan na son dan gaban Arsenal Folarin Balogun
Inter Milan na son dan gaban Arsenal Folarin Balogun

Brighton

Brighton ta amince da yarjejeniyar dan tsakiyar Ajax dan kasar Ghana, Mohammed Kudus, mai shekara 23, a kan kudi fam miliyan 34 da dubu dari biyar. (Athletic – subscription required)

Manchester City

Manchester City na duba yiwuwar sayen dan bayan Spaniya Aymeric Laporte, mai shekara 29, bayan ta dauki dan bayan Croatia Josko Gvardiol daga RB Leipzig. (Mirror)

Tottenham

Shugaban Tottenham Daniel Levy, ya yi watsi da wa’adin da Bayern Munich ta ba shi a kan ya yanke shawara a kan tayin da ya yi wa dan gaban Ingila Harry Kane na fam miliyan 86. (Bild – in German)

Aston Villa

Dan wasan gefen Aston Villa Jaden Philogene, mai shekara 21, ya zama dan wasan da Liverpool ta sa a gaba. (Liverpool Echo)

Newcastle

Newcastle na tattauna wa da wakilin dan gaban Galatasaray Nicolo Zaniolo, mai shekara 24, to amma AC Milan da Juventus suma na sha’awar dan wasan dan kasar Italiya. (Chronicle)

Bayer Leverkusen

Yanzu dan bayan Bayer Leverkusen Edmond Tapsoba, mai shekara 24, baya cikin wanda Tottenham ke nema, bayan da ta mayar da hankali wajen daukar dan tsakiyar Wolfsburg, Micky van de Ven, mai shekara 22 . (Yahoo)

Chelsea

Chelsea ta amince da ka’idojin da aka shimfida mata a kan dan wasan gefen Faransa Michael Olise, mai shekara 21, bayan ta yi wa Crystal Palace ta yinfan miliyan 26 a kan ɗan wasan. (Metro)

Za a bar dan wasan Ingila da ke buga wasan ‘yan kasa da shekara 21 Lewis Hall, ya bar Chelsea a kan aro inda zai koma Crystal Palace. . (90 min)

Nottingham Forest

Nottingham Forest ta fara tattauna wa da Nice a kan komawar mai tsaron ragar Denmark Kasper Schmeichel. (Nottingham Post)

Everton

Everton da West Ham da kuma Crystal Palace na sa ido a kan dan bayan Ingila Trevoh Chalobah, mai shekara 24, yayin da Chelsea ta ba shi damar barin kungiyar a kakar bana. (Yahoo)

Burnley

Burnley ta cimma yarjejeniya da Ajax a kan aron dan gaban kungiyar dan kasar Denmark Mohamed Daramy. (Athletic – subscription required)

Danna Nan: Barcelona na son Bernado Silva 2023

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button