Labarai

Jami’an tsaron OPERATION FARAUTA 1 sunyiwa matashi dukan tsiya har Allah ya dauki ransa

Jami’an tsaron OPERATION FARAUTA 1 sunyiwa matashi dukan tsiya har Allah ya dauki ransa

Sunan Matashin

Sunan matashin Abdullahi Tukur Abba, dan jihar Adamawa wanda jami’an tsaron “Operation Farauta” suka mishi dukan tsiya har Allah ya dauki ransa.

Dalili

Da farko an zargi matashin da sace waya iPhone 7 a gidan makwabcinsu dake unguwar Wuro Chakke, makwabcin ya kira jami’an “Operation Farauta” suka dauke shi suka je suka mishi dukan tsiya har ya fita daga hayyacinsa.

Suka dawo dashi gidansu daure da ankwa jina-jina domin ya nuna musu inda ya boye wayar.

Da suka shigo dashi gidan, sai Abdullahi ya fadawa mahaifinshi cewa, shi bai dauki wayar ba, kawai ya amsa musu ne domin ya ceci rayuwarshi, saboda suna shirin kashe shi da duka.

Bayan an chaje gidan ba’a samu wayar ba sai Abdullahi ya fadi kasa yana aman jini, take mahaifinshi ya kaishi asibiti, likitoci sun shaidawa iyayan yaron da cewa dukan da aka mishi an fasa mishi har marenansa, wanda shine yayi sanadiyar rasuwarshi.

Sai daga baya aka gano cewa ba Abdullahi ne ya saci wayar ba.

Hakika an zalunci Abdullahi, fiye da wuce kima, Abdullahi matashin yaro ne a wannan shekarar ya kammala sakandiri.

Muna kira ga Gwamnatin

Muna kira ga Gwamnatin jihar Adamawa karkashin jagorancin Gwamnan jihar Adamawa Governor Ahmadu Umaru Fintiri da hukumar ‘yan sanda ta jihar, da su gaggauta daukan mataki akan wa ‘yanda suka zalunci Abdullahi, don gudun kara aukuwar irin hakan anan gaba.

Wallahi nayi matukar tausayawa wannan matashin, Don Allah mu taimaka da Sharing har sakon ya isa ga Gwamnatin jihar domin daukan mataki akan su, domin sun zalunci Abdullahi.

Jami'an tsaron OPERATION FARAUTA 1 sunyiwa matashi dukan tsiya har Allah ya dauki ransa
Jami’an tsaron OPERATION FARAUTA 1 sunyiwa matashi dukan tsiya har Allah ya dauki ransa

Amma mizakace dangane da wannan lamarin.

Danna Nan:Ahmad Musa Ya taimake ɗan Film baba karkuzu da maƙuddan

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Fac Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button