Labarai

Labaran Wasanni Kwallon ƙafa 3 Da suka Girgiza Duniya

Labaran Wasanni Kwallon ƙafa 3 Da suka Girgiza Duniya

(1)SADIO MANE YA KOMA AL-NASSR TA SAUDI ARABIA

Bayern Munich ta sanar cewar tsohon dan kwallon Liverpool, Sadio Mane ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia.

Dan wasan tawagar Senegal, ya ci kwallo 12 a karawa 38 da ya yi wa kungiyar Jamus, wadda ta lashe Bundesliga a kakar da ta wuce.

Babban jami’in Bayern, Jan-Christian Dreesen ya ce dan kwallon mai shekara 31 ya ci karo da kalubale tun bayan da ya koma Jamus daga Anfield.

Mane zai koma taka leda tare da Cristiano Ronaldo a Al-Nassr kan fam miliyan 35 kamar yadda ake hasashe.

Irin kudin da Bayern Munich ta dauki Mane a bara kenan daga kungiyar da ke Anfield.

Al-Nassr ta dauki Ronaldo a Disamba, sannan ta dauki dan wasan Croatia, Marcelo Brozovic da na Brazil, Alex Telles da na Ivory Coast, Seko Fofana.

(2)FULHAM ZA TA DAUKI DEMARAI GRAY DAGA EVERTON

Fulham tana tattaunawa da dan kwallon tawagar Jamaica, Demarai Gray, daga Everton.

Gray mai shekara 27, ya koma kungiyar da ke Goodison Park daga Bayer Leverkusen kan fam miliyan 1.7 a 2021, wanda ya yi mata wasa 75 da cin kwallo 12.

Crystal Palace,da kungiyar Turkiya Besiktas da wasu daga Saudiyya na son daukar Gray.

HAUSAONE ta fahimci cewar Fulham na son daukar Gray domin ta kara karfin kungiyar, don fuskantar kakar bana da za a fara cikin Agustan 2023.

Gray, tsohon dan kwallon Leicester City ya koma yin atisaye, bayan da ya fafata a gasar Concacaf Gold Cup.

Fulham tana da gurbi bayan da Manor Solomon ya koma Tottenham, sannan Dan James ya sake komawa Leeds United.

Kawo yanzu Fulham ta dauki Raul Jimenez daga Wolverhampton da Calvin Bassey daga Ajax a bana.

Wasu rahotanni na cewar Fulham ta kulla yarjejeniyar sayen dan wasan Juventus mai tsaron baya, Luca Pellegrini.

(3)KO MBAPPE ZAI KOMA CHELSEA?

Rahotanni sun ce kungiyar Paris St-Germain ta bai wa Kylian Mbappe wa’adin sabunta kwantiragi a ranar 1 ga watan Agusta ko kuma ya bar kungiyar.

Ana rade-radin cewa dan wasan na Faransa, mai shekara 24, ya amince ya koma Real Madrid a kakar wasa mai zuwa a kyauta idan kwantiraginsa a PSG ya kare.

Mbappe na damar barin PSG a kakar bana – ko dai a matsayin aro ko kuma a kan kwangilar dindindin, wanda ta hakan ne PSG za ta iya samun kudi a kansa.

Sai kuma yanzu ga Chelsea da Barcelona na nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan.

A cewar wata majiya, mamallakin Chelsea, Todd Boehly, yana son Mbappe amma yana fuskantar gogayya daga Barcelona inda kungiyoyin biyu ke da niyyar bayar da ‘yan wasa da kuma tsabar kudi.

Danna Nan: PSG za ta sayi Ousmane Dembele daga Barcelona, Bayern Munich na son David Raya

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Labaran Wasanni Kwallon ƙafa 3 Da suka Girgiza Duniya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button