Labarai

Lionel Messi ya ci kwallo biyu a wasan Inter Miami

Lionel Messi ya ci kwallo biyu a wasan Inter Miami

Acikin shirin namu nayau zakuji cewaLionel Messi ya ci gaba da taka rawar gani a Inter Miami inda ya zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Orlando City 3-1 a gasar cin kofin League a ranar Laraba.

Kwallaye biyu da dan wasan mai shekaru 36 ya ci sun taimaka wa kungiyarsa wurin samun nasarar zuwa zagayen gaba 16 a gasar , wadda ake bugawa tsakanin ƙungiyoyin da ke Major League Soccer na Amurka da kuma La Liga MX na Mexico.

Miami dai ba ta yi nasara ba a wasanni 11 kafin zuwan Messi, amma yanzu sun yi nasara a wasanni ukun da suka yi a jere.

Tsohon abokin wasan Messi na Barcelona, ​​Jordi Alba, ya fara buga wasansa na farko a Miami, inda ya shiga wasan a minti na 64 da fara wasa.

Tsohon abokin aikinsu na Camp Nou Sergio Busquets shi ma ya koma buga gasar ta MSL, yayin da tsohon kocin Barca da Argentina Tata Martino ke jagorantar kungiyar bayan ya maye gurbin Phil Neville a kungiyar.

Lionel Messi ya ci kwallo biyu a wasan Inter Miami

Danna Nan: PSG za ta sayi Ousmane Dembele daga Barcelona, Bayern Munich na son David Raya

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button