Labarai

Makomar: Guimaraes, Firmino, Pochettino, Milinkovic-Savic

Makomar: Guimaraes, Firmino, Pochettino, Milinkovic-Savic

Barcelona na son sayen dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes, amma kungiyar za ta bada kudin sayan kusan euro miliyan 100 (£87m) don shawo kan Newcastle United ta sayar da dan wasan mai shekaru 25. (KUNDINWASANNI)

Real Madrid na tunanin fara zawarcin dan wasan gaban Brazil Roberto Firmino, mai shekara 31, wanda zai zama wakili na kyauta idan kwantiraginsa na Liverpool ya kare a bazara. (KUNDINWASANNI)

Tsohon kocin Tottenham da Paris St-Germain Mauricio Pochettino, mai shekara 51, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku don zama sabon kocin Chelsea. (KUNDINWASANNI)

Har yanzu Brazil na fatan ganin kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya zama kocinta na gaba. Kasar wadda ta Lashe Kofin duniya sau biyar sun kasance ba tare da koci ba tun bayan da Tite ya bar gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a watan Disamba. (KUNDINWASANNI)

Liverpool za ta iya sayen dan wasan tsakiyar Lazio Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 28, kan Yuro miliyan 26 (£22.5m) kwantiragin dan kasar Serbia zai kare a shekarar 2024. (KUNDINWASANNI)

Damar Manchester United na siyan dan wasan baya na Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekara 26, da kuma dan wasan Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 24, daga Napoli ya kara karfi, a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan makomar kocin Italiya Luciano Spalletti. (KUNDINWASANNI)

Newcastle United kuma ta shiga zawarcin Kim na Napoli. (KUNDINWASANNI)

Sheffield United na ci gaba da bin diddigin dan wasan Nottingham Forest dan kasar Ingila Lewis O’Brien, mai shekara 24, wanda a halin yanzu yake zaman aro a DC United. (KUNDINWASANNI)

Crystal Palace na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan tsakiya na Bournemouth da Colombia Jefferson Lerma, mai shekara 28, a karshen kakar wasa ta bana. (KUNDINWASANNI)

Dan wasan gaba na Chile Alexis Sanchez, mai shekara 34, yana sha’awar komawa gasar Premier bayan ya taka leda a Arsenal da Manchester United bayan zamansa a Marseille. (KUNDINWASANNI)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button