Labarai

Manchester United na tattaunawa kan dan wasan karasar Morocco Sofyan Amrabat

Manchester United na tattaunawa kan dan wasan karasar Morocco Sofyan Amrabat

Manchester United na kokarin sayen dan wasan gaba, kuma ana alakanta su da dan wasan tsakiya na Morocco Sofyan Amrabat.

A cewar shafin intanet na kwallon kafa 90min, United na ci gaba da tattaunawa da Fiorentina kan dan wasan tsakiyar Morocco mai shekaru 26 yayin da suke kokarin sayar da Fred dan Brazil mai shekaru 30 daga kungiyar.

An fahimci cewa United na neman kara karfin tsakiyarta, kuma ta bude tattaunawa da Fiorentina kan Amrabat, wanda ya taimaka wa kulob dinsa zuwa wasan karshe a gasar cin kofin Europa a bara, kuma ya kasance fitaccen dan wasa a Morocco a gasar cin kofin duniya ta 2022.

Har ila yau United na aiki wajen ganin ta sallami wasu daga cikin ‘yan wasanta, kuma ana samun ci gaba dangane da sayar da Fred ga kungiyar Galatasaray ta Turkiyya.

Tafiyar dan Brazil din za ta kawo sauki kan lissafin albashin United, kuma bayan da ta yi watsi da tayin Farko da Galatasaray ta yi ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

United ta riga ta kulla yarjejeniya da Mason Mount da Andre Onana a kan manyan kudade a bazara – yunkurin da aka yi na karfafa kungiyar ta United kafin komawa gasar zakarun Turai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button