Labarai

Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Juyin mulki

Acikin shirin namu nayau zakuji cewa tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi ranar 26 ga watan Yuli, ga alama Nijar ta ƙara tsunduma cikin matsalolin tsaro.

Hare-haren masu iƙirarin jihadi da zaman zulumi kan yiwuwar fuskantar matakin amfani da ƙarfin rundunar ko-ta-kwana daga Ecowas.

A baya-bayan nan masu iƙirarin jihadi sun kai harin da ya yi sanadin kashe sojojin ƙasar 17 ranar Talatar da ta wuce a yankin Tillaberi.

Haka zalika, an kashe fararen hula duk dai a wannan rana aƙalla 31 a wasu hare-hare daban duk dai a cikin iyaka uku mai ƙaurin suna ta jihar Tillaberi.

Su ne mafi muni a jerin sabbin hare-hare da Nijar ta fuskanta, tun bayan hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed daga mulki.

A Yamai, matasa ‘yan aikin sa-kai ne da suka ɓulla don taya hukumomi aikin zaƙulo ɓata-gari da katse hanzarin shiga da makaman da za a yi amfani da su wajen yaƙar Nijar ne, suka fara zama alaƙaƙai ga mazauna babban birnin.

Akwai dai zarge-zargen cewa wasu na fakewa da aikin wajen tafka sace-sace da kuma cin zarafin masu ababen hawa waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Sai dai, ga alama babban abin da ya fi damun masu mulki a fadar shugaban ƙasa, yana can nisan ɗaruruwan kilomitoci a tsalaken iyakokin Nijar da wasu maƙwabtanta, kamar Jamhuriyar Benin da Najeriya.

Rundunar ko-ta-kwana ta Ecowas

Da sanarwar da Ecowas ta bayar a ranar Juma’a cewa manyan hafsoshin tsaron ƙungiyar sun tsaida ranar tura dakaru cikin Nijar, hukumomin ƙasar mai yiwuwa ne su ƙara mayar da hankali wajen ƙarfafa dakarun da za su katse hanzarin rundunar Ecowas.

Sojojin da suka yi juyin mulki, a cewar rahotanni sun janye dakarun sojojin ƙasar masu yawa daga fagen daga daban-daban, inda suka dawo da su babban birnin Niamey.

Sabbin shugabannin mulkin Nijar sun ƙi jin kashedin Ecowas na cewa su tsame hannunsu daga harkokin mulki su koma bariki. Ƙungiyar ƙasashen dai ta yi barazanar tura rundunarta ko-ta-kwana don auka wa Nijar, da nufin dawo da mulkin dimokraɗiyya.

Babu masaniya a kan yawan sojoji da kayan yaƙin da Ecowas za ta aika Nijar. Amma a yayin taron da manyan hafsoshin ƙungiyar suka kammala ranar Juma’a a Accra, jami’an ƙungiyar sun ce ƙasashe guda tara da suka halarci taron duk sun yi alƙawarin ba da gudunmawar dakaru da kayan yaƙi don auka wa Nijar, matuƙar ƙoƙarin diflomasiyya ya faskara.

Mai yiwuwa ne kuma, Ecowas ta samu taimako daga ƙasashen ƙetare aƙalla na bayanan sirri.

Sojoji masu mulkin Nijar dai, na samun goyon baya ne daga maƙwabtansu Mali da Burkina Faso.

Sun yi alƙwarin cewa ɗaura yaƙi da Nijar, da zimmar dawo da hamɓararren shugaban ƙasar, tamkar shelar yaƙi ce a kansu. Sai dai duk wani taimakon soja da za su bai wa Nijar, mai yiwuwa ne ya zama ragagge, saboda su ma suna fama da ɗumbin matsalolin tsaro da ya addabe su a gida.

Rikicin ‘yan ta-da-ƙayar-baya ya sa ya tagayyara su, kuma zai sa duk wani tallafi da za su bai wa wani, to zai kasance ba wanda zai jefa tsaron ƙasashen cikin ƙarin hatsari ba ne.
Kamar Mali da Burkina Faso, ƙasashen Ecowas ma kamar Najeriya suna da nasu ɗumbin matsalolin tsaro a cikin gida. Kuma tamkar Nijar, har yanzu Najeriyar ba ta gama farfaɗowa daga rikicin Boko Haram ba.

Haka zalika, majiyoyi a baya-bayan nan na nuna cewa Nijar ta ƙara yawan dakarunta a kan iyakokinta da Najeriya da kuma Jamhriyar Benin, da nufin kare ƙasar daga sojojin mamaya na Ecowas.

Kafar yaɗa labarai ta Maliactu da ke ƙasar Mali ta ba da rahoton cewa “A garin Gaya, na kan iyaka tsakanin Benin da Najeriya, ana ganin kai-komon dakarun Nijar ba dare ba rana. Al’ummar yankin, ba tare da wata fargaba ba, suna fita su jinjinawa da dakarun sojojin da ake turawa”.

Kafar ta ƙara da cewa a yankin Ƙonni, hukumomin Nijar sun tura dakaru yayin da mazauna yankin ke ci gaba da gudanar da harkokin rayuwa kamar yadda suka saba.

Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki
Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Rikicin masu iƙirarin jihadi

‘Yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi a yankin iyaka uku na Tillaberi a baya-bayan nan ya ƙara tsananta da hare-haren ta’addanci.

A cikin abin da bai fi kwana 20 ba, mayaƙa masu alaƙa da IS da Al-Qaeda sun kashe sojojin Nijar fiye da arba’in a jerin hare-hare guda takwas da suka kai.

Masharhanta sun ce an shafe tsawon lokaci, ba a ga yawan kai hare-hare irin wannan ba a jihar Tillaberi. Haka zalika, harin baya-bayan nan na ranar Talata, wanda ya yi sanadin kashe soja 17 a wani kwanton-ɓauna, shi ne mafi muni a cikin hare-haren.

Kwana uku kafin sannan, wasu mahara sun yi kwanton-ɓauna ga wani ayarin sojojin rundunar tsaron ƙasa ta Sanam da ke sintiri, inda suka kashe mutum shida.

Ƙaruwar hare-haren sun janyo ƙarin matsin lamba kan shugabannin juyin mulkin Nijar, waɗanda suka kafa hujja da taɓarɓarewar tsaro wajen hamɓarar da Shugaba Bazoum.

Tsaron cikin gida

Ɓullar ƙungiyoyin matasa ‘yan sa-kai a biranen Nijar, kamar Yamai ya zama sanadin sanya damuwa a zukatan mazauna birnin. Ana zargin wasu ɓata-gari da fakewa da matasan wajen aikata sace-sace da cin zarafin masu ababen hawa.

Wani ɗan ƙungiyar farar hula, Mallam Surajo Isah ya shaida wa BBC cewa suna samun ƙorafe-ƙorafe daga wajen mazauna birnin Yamai kan yadda matasa ‘yan sa-kai suke tonon asiri da wulaƙanta mutane da tozarta.

“Da sata da ma ƙone-ƙonen dukiyoyin al’umma.”

Ya ce ba daidai ba ne mutanen da suka fito suka ce za kare doka da oda, amma su ɓuge da aikata abubuwan da za su jefa rayuwar mutane cikin ƙunci da fargaba

“Sun tayar ma mutane hankali, mutane suna cikin ɗar-ɗar, suna cikin tsoro.”

Mallam Bana Ibrahim, ɗaya daga cikin jagororin ‘yan sa-kan ya ce suna ba da gudunmawa ne wajen gudanar da bincike kan ababen hawa don ganin wasu miyagun mutane ba su yi fasa-ƙwaurin makamai zuwa cikin ƙasar ba.

Ya ce a duk lokacin da suka ga ɓata-gari a cikinsu, suna ƙwace makamansu, kuma su damƙa su hannun hukumomi.

Wani mazauni birnin mai suna Mallam Jamilu ya ce shugaban mulkin soja Janar Tchiani ya yi alƙawari kare rayuka da dukiyar al’ummar ƙasa, bayan ya karɓi mulki, don haka bai kamata hukumomi su yi sakacin bai wa wasu tsirarun matasa damar keta ‘yancin jama’a ba.

Ya yi kira ga mahukunta su ɗauki mataki don gudun ƙazancewar lamarin. A cewarsa, Nijar ba ta yi lalacewar da za a bar wasu tsiraru waɗanda ya kira ‘yan tasha suna tafka ta’asa da suna kare al’umma ba.

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Danna Nan: Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button