News

Napoli ta yi watsi da tayin PSG na £100m kan Osimhen, Man city ta taya Rice kan £90m

Napoli ta yi watsi da tayin PSG na £100m kan Osimhen, Man city ta taya Rice kan £90m

West Ham ta karɓi tayi daga Manchester City da ke son saye ɗan wasan tsakiya na Ingila, Declan Rice mai shekara 24 kan fam miliyan 90. (The Athletic)

Napoli ta yi watsi da tayin Paris St-Germain na yuro miliyan 100 kan ɗan wasanta asalin Najeriya Victor Osimhen mai shekara 24. Kungiyoyi irinsu Liverpool da Manchester United da Newcastle duk na zawarcinsa. (Gazzetta dello Sport – in Italian)

Tottenham na shirin gabatar da tayin fam miliyan 40 kan ɗan wasan Leicester James Maddison – amma ita kungiyar fam miliyan 60 take nema kan ɗan wasan mai shekara 26. (Telegraph – subscription required)

Bayern Munich na zawarcin Harry Kane na Tottenham mai shekara 29, ɗan wasan dai ya nuna sha’awar tafiya Jamus. (Sky Sport Germany)

Newcastle ta yi nisa a tattaunawar cimma yarjejeniya da ɗan wasan Southampton Tino Livramento. (Telegraph – subscription required)

‘Yan wasan Ingila biyu Jadon Sancho da Harry Maguire na cikin jeren ‘yan wasa 13 da Manchester United ke shirin sayarwa a wannan kaka. (Mail)

Da alama burin Manchester United ba lallai ya cika ba, bayan kwashe tsawon lokaci na zawarcin Adrien Rabiot da ke shirin sabunta zamanta a kungiyar Serie A ta Juventus. (Corriere dello Sport – in Italian)

Mohamed Salah ba shi da niyyar barin Anfield a yanzu duk da raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan yiwuwar ya bar kungiyar zuwa Saudiyya. (Mirror)

Sai dai a yanzu, tsohon abokin Salah da suka buga wasa tare a Liverpool, Alex Oxlade – Chamberlain mai shekara 29, na nazari kan ko ya karɓi tayi mai gwaɓi da aka gabatar masa daga Saudiyya.(Mail)

Arsenal ta sanya sunan Youssouf Fofana, mai shekara 24, a jeren ‘yan wasan da za ta iya ɗaukowa idan ba ta yi nasara daidaitawa da ɗan wasan tsakiya na West Ham ba, Declan Rice. (L’Equipe – in French, subscription required)

AC Milan za ta saye ɗan wasan Ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 27, daga Chelsea kan yuro miliyan 15. (Calciomercato – in Italian)

Kocin Aston Villa Unai Emery na son sayo ɗan wasan Sifaniya Pau Torres, mai shekara 26, kan fam miliyan 51.5. (Times – subscription required)

Sheffield United na tattaunawa mai zurfi da ɗan wasan Ingila Mason Holgate, mai shekara 26, da ke zaman aro a Everton. (talkSPORT)

Liverpool ta bi sahun Arsenal a zawarcin Romeo Lavia, mai shekara 19, daga Southampton. (Fabrizio Romano)

Kungiyar Bundesliga ta Wolfsburg na neman fam miliyan 26 kan ɗan wasan Netherlands Micky van de Ven, 22, da ake alakantawa da Tottenham. (Evening Standard)

Ɗan wasan Sunderland Chris Rigg, mai shekara 16, ya yi watsi da tayin da ya samu daga

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button