Labarai

Sai bayan shekara 3 zamu mika mulki ga farar hula a Nijar

Sai bayan shekara 3 zamu mika mulki ga farar hula a Nijar

Acikin Shirin namu nayau zakuji cewa Sai nan da shekara uku za mu mika mulki ga farar hula a Nijar cewar Tchiani.

Shugaban gwamnatin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce sojojin kasar za su mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da shekaru uku masu zuwa.

Janar Abdourahmane Tchiani lokacin da yake gabatar da jawabi ta kafat talibijin, ranar 28 ga watan Yuli, 2023, bayan hambarar da zababben shugaban kasar Muhammad Bazoum. AP

Janar

Janar din ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka yada a gidan talabijin din kasar a daren ranar Asabar.

Tchiani

Tchiani ya bayyana hakan ne bayan ganawa da tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya.

Sai bayan shekara 3 zamu mika mulki ga farar hula a Nijar
Sai bayan shekara 3 zamu mika mulki ga farar hula a Nijar

Janar Tchiani

Janar Tchiani ya ce nan da wata guda, gwamnatin mulkin soji za ta kafa wani kwamiti da zai yi nazari tare da kafa sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Yayin da ya ci gaba da cewa Nijar ba ta son shiga yaki, inda ya ce karamar kasar za ta kare kanta idan bukatar hakan ta taso.

Table of Contents

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Idan Kanada labarin da akeso a wallafa acikin wannan shafin namu mai albarka,zaka iya yimuna comments ta wajenda munka tanadarmuku.

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook1 Page

  1. ↩︎

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button