Labarai

Sojojin Ecowas zasu shiga tattaunawa don tsara shirin tunkarar Nijar

Sojojin Ecowas zasu shiga tattaunawa don tsara shirin tunkarar Nijar

Manyan hafsoshin sojin Ecowas za su gana don tsara shirin tunkarar Nijar

Manyan hafsoshin sojin Afirka ta Yamma za su gudanar da taro a ‘yan kwanaki masu zuwa don tsara shirye-shirye kan yiwuwar amfani da ƙarfin soja, yayin da ƙasashen duniya ke ƙara nuna fargaba game da yanayin da ake tsare da hamɓararren Shugaba Bazoum Mohamed.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce taron manyan hafsoshin sojin na nuna cewa ƙasashen Afirka ta Yamma suna gaggauta shirye-shiryen tura sojoji da yiwuwar ɗaukar matakin kawar da masu juyin mulki a Nijar.

“Ana tsara yin wani (taron) a makon gobe,” Reuters ya ambato wani mai magana da yawun Ecowas yana cewa.

Sojojin Ecowas zasu shiga tattaunawa don tsara shirin tunkarar Nijar
Sojojin Ecowas zasu shiga tattaunawa don tsara shirin tunkarar Nijar

Jami’in gwamnatin Najeriya

Wani jami’in gwamnatin Najeriya da kuma wata majiyar sojojin Kwatdebuwa sun ce za a yi taron ne ranar Asabar a Ghana.

Zuwa yanzu babu masaniya ƙarara kan yadda girman rundunar zai kasance, da tsawon lokacin da za a shafe kafin a iya tattaro dakarun, da kuma idan haƙiƙa rundunar za ta auka don yin mamaye.

Ƙungiyar Ecowas

Ƙungiyar Ecowas dai ta ce har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke kuma tana fatan za a iya cimma masalaha cikin lumana.

Masu sharhi kan al’amuran tsaro kuma sun ce dakarun Ecowas na iya kwashe tsawon makonni ko fiye da haka, kafin su haɗu, abin da mai yiwuwa zai ba da dama ga ƙoƙarin tattaunawa.

Kwatdebuwa ce kaɗai ƙasar da ya zuwa yanzu ta bayyana adadin dakarun da za ta aika.

Alassane Ouattara

Shugaba Alassane Ouattara ya yi alƙawari a ranar Alhamis cewa ƙasarsa za ta aika wata bataliyar sojoji da ta kai yawan mutum 850 – 1,100.

Juyin mulki

Hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum ya kasance juyin mulki na bakwai a Yammaci da Tsakiyar Afirka cikin shekara uku, abin da kuma ya ƙara jefa yankin cikin tunzuri, baya ga hare-haren masu iƙirarin jihadi da yake fama da su tsawon lokaci.

Domin ƙarin bayani:labari

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Danna Nan: Yanda ake sukar tinubu akan yunƙurin tura sojoji Nijar

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button