Labarai

Super Falcons ta ci Australia 3-2 A Gasar kofin duniya 2023/2024

Super Falcons ta ci Australia 3-2 A Gasar kofin duniya 2023/2024

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta doke ta Australia da ci 3-2 a wasa na biyu a cikin rukuni da suka kara ranar Alhamis a gasar cin kofin duniya ta mata.

Mai masaukin baƙi, Austalia ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Emily van Egmond bayan da ta samu tamaula ta hannun Caitlin Foord.

Sai dai kuma Najeriya ta farke daf da za a tashi ta hannun Uchenna Kanu,.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Super Falcons ta farke ta hannun Osinachi Ohale.

Asisat Oshoala ce ta ci na uku, bayan da ƴan wasan Australia Alanna Kennedy da Mackenzie Arnold suka yi kuskure.

Daga baya Australia ta zare ɗaya ta hannun Kennedy, inda Najeria ta yi nasara da cin 3-2.

Da wannan sakamakon Najeria tana jan ragamar rukuni na biyu da maki hudu, Australia ta biyu mai maki uku.

Ranar Litinin Super Falcons za ta buga wasa na uku a cikin rukuni da Jamhuriyar Ireland, wadda tuni aka ci wasa biyu.

A ranar ce Australia za ta fafata da Canada a daya karawar rukuni na biyu a gasar kofin duniya ta mata da ake yi a Australia da New Zealand.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button