Labarai

Tinubu yace baza’a ƙara farashin man fetur ba

Tinubu yace baza’a ƙara farashin man fetur ba

Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa ƴan ƙasar tabbacin cewa ba za a ƙara farashin man fetur ba.

Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, wanda ya bayar da tabbacin ya ce a yanzu babu shirin ƙara farashin man fetir ɗin.

“Yau Talatada safe na samu ganawa da Shugaba Tinubu. Mun tattauna kan abubuwan da ke faruwa a ƙasa game da man fetir,” a cewarsa.

“Shugaban ƙasa yana jaddada matsayar kamfanin mai na ƙasa NNPCL cewa ba za a ƙara farashin man fetir ba yanzu. Muna ƙara jaddada hakan.”

Kakakin ƙungiya

Tinubu yace baza'a ƙara farashin man fetur ba
Tinubu yace baza’a ƙara farashin man fetur ba

Kakakin ƙungiyar dillalan man fetir ta Najeriya Chief Chinedu Ukadike ne ya fara tsegunta batun ƙarin farashin man, inda ya ce ƴan Najeriya su tsammaci tashin farashin mai saboda rashin daidaiton darajar naira a kasuwar canjin kuɗi.

Ƙungiyoyin ƙwadago

Lamarin ya haifar da ruɗani tsakanin jama’ar ƙasar, har ya kai ga ƙungiyoyin ƙwadago sun yi barazanar shiga zanga-zanga.

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Danna Nan: Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button