Labarai

Tinubu yace yasan ƙuncin da janye tallafin mai ya jefa ƴan Najeriya

Tinubu yace yasan ƙuncin da janye tallafin mai ya jefa ƴan Najeriya

Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su ɗan ƙara sadaukar da kansu domin ceto ƙasar daga durƙushewa.

Jawabin Tinubu

A cikin jawabinsa na tunawa da Ranar Dimokraɗiyya wadda ake yi duk ranar 12 ga watan Yuni, shugaba Tinubu ya ce ya san cewa matakin janye tallafin man fetur, zai haddasa ƙarin wahala ga talakan Najeriya.

Ya ce “ina jin irin raɗaɗin da kuke ji”.

Sai dai in ji shi, wannan mataki ne da dole sai an ɗauka domin ceto Najeriya daga durƙushewa da kuma ƙwato dukiyar ƙasar daga hannun wasu tsirarun mutane marasa kishi.

Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa haƙurinsu ba zai tafi a banza ba, bisa la’akari da yarda da kuma amanar da suka bai wa gwamnatinsa.

Manufar gwamnatin Tinubu

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin da yake jagoranta za ta biya ‘yan Najeriya da gagarumin ƙoƙari wajen zuba kuɗi a harkokin sufuri da bunƙasa ilmi da kuma samar da wutar lantarki, baya ga ƙoƙarin bunƙasa kula da lafiya da sauran kayan amfanin al’umma.

A cewar sabon shugaban, gwamnatinsa za ta yi hakan ne don inganta rayuwar miliyoyin ‘yan Najeriya.

Alƙawarin da Tinubu ya ɗauka

Shugaban ya dai yi alƙawarin ƙara ƙwazo don cika dukkan alƙawurran da ya ɗaukarwa ‘yan ƙasar a lokacin yaƙin neman zaɓe bisa abin da ya kira manufar ‘Sabunta Fata’ wato Renewed Hope.

Tinubu ya ce tsarin dimokraɗiyyar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Moshood Abiola ya mutu yana gwagwarmayar tabbatarwa a Najereiya, shi ne wanda zai fifita da kuma kyautata jin daɗin al’umma a kan muradin ƙashin kai na shugabanni.

Sannan kuma da tsarin da mutanen da ake mulka za su iya cimma burin rayuwa kuma su samu farin ciki.

Bola Ahmed Tinubu a cikin jawabin nasa ya nunar cewa shekara 30 kenan cif tun lokacin da ‘yan Najeriya suka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a 1993 don komawa ga tsarin dimokraɗiyya daga mulkin sojoji ‘yan kama-karya.

Kafin wata dokar soja ta rusa zaɓen 12 ga watan Yuni da ya bai wa Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola na jam’iyyar SDP nasara.

Ya ce a kowacce rana irin wannan, tsawon shekaru Najeriya za ta ci gaba da tunawa da MKO Abiola da kuma sauran gwarazan dimokraɗiyyar ƙasar kamar mai ɗakin marigayin Hajiya Kudirat Abiola wadda cikin zalunci aka yi mata kisan gilla lokacin da take gwagwarmayar tabbatar da ‘yancin talaka.

Sai kuma Pa Alfred Rewane, ɗaya daga cikin gwarazan samun ‘yancin Najeriya da kuma Manjo Janar Shehu Musa ‘Yar’adua wanda sojoji masu mulki suka rufe wa baki a lokacin da yake fafutukar tabbatar da mulkin dimokraɗiyya.

A cewar Tinubu, irin waɗannan gwaraza, sun sadaukar da “‘yancinsu ne a jiya don rayuwarmu ta yau”.

Game da zaɓen Tinubu 2023

Ya ce a wannan shekara an gudanar da zaɓuka waɗanda suka zama al’ada ga tsarin dimokradiyyar Najeriya tun bayan komawa kan tafarkin siyasa a 1999.

A cewarsa, zafin fafatawar da aka samu a zaɓen shi kansa wata shaida ce cewa dimokraɗiyya ta kafu kuma tana ci gaba da bunƙasa a ƙasar.

Tinubu ya ce tun fil’azal da ma mutanen da suka yi nasara sukan yi murna da farin ciki, yayin da waɗanda suka faɗi sukan ji ɓacin rai da takaici.

Sai dai daɗin tsarin dimokraɗiyya shi ne waɗanda suka yi nasara a yau, suna iya yin rashin nasara gobe, yayin da waɗanda suka faɗi yau, suna da wata dama ta sake tsayawa takara har ma su ci zaɓe a wani zagaye.

Tinubu yace yasan ƙuncin da janye tallafin mai ya jefa ƴan Najeriya
Tinubu yace yasan ƙuncin da janye tallafin mai ya jefa ƴan Najeriya

In ji shi, waɗanda ba za su iya daurewa, su karɓi kaddara da zafin faɗuwa zaɓe ba, ba su cancanci murnar samun nasara ba, idan lokacinsu ya zo suka ci zaɓe.

Haka zalika, Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin tabbatar da gaskiya da daidaito da kuma adalci.

Ya kuma yi alƙawarin tabbatar da aiki da ikonsa da kuma nauyin da al’umma ta ɗora masa wajen yin mulki cikin adalci da mutunta doka.

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Danna Nan: Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button