Labarai

Tunibu ka ba mu kunya buɗaɗiyar wasiƙa daga shugaban APC

Tunibu ka ba mu kunya buɗaɗiyar wasiƙa daga shugaban APC

Shugaba a APC

Shugaba a APC Ya Rubutawa Bola Tinubu Wasika, Ya ce ‘Ka Ba Mu Kunya’ a Mulki.

Mohammed Lukman ya aika budaddiyar wasika zuwa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu Jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya na ganin ba gwamnatin tarayya ba ta fara da kafar dama ba Bayan tsaida tikitin musulmi da musulmi a zaben 2023, Lukman yake cewa an musuluntar da NWC

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Salihu Mohammed Lukman ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Bola Ahmed Tinubu.

Salihu Mohammed Lukman ya na cewa ba haka aka yi tsammani daga Bola Tinubu da ya hau mulki a Mayu ba.

Alhaji Salihu Mohammed Lukman ya fadawa Mai girma shugaban Najeriya cewa alamu sun fara nuna gwamnati mai-ci ta fara da kafar hagu.

Tinubu

Musulmi da Musulmi a NWC A cewar ‘dan siyasar, majalisar gudanarwa watau NWC ta APC ta samu kan ta a irin yanayin da jam’iyyar ta shiga na tikitin musulmi da musulmi.

Goyon bayan Abdullahi Umar Ganduje da Ajibola Bashiru su ka samu daga shugaban kasar ya jawo shugabancin APC ya na hannun musulmai biyu.

Business Day ta ce Lukman ya ce zargin da ake yi wa jam’iyyar na maida kiristoci saniyar ware ya jawo rashin jituwa a APC da kuma cikin al’umma.

Baya ga haka, tsohon shugaban jam’iyyar ya ce Bola Tinubu ya ki kyale Umaru Tanko Al-Makura ko wani a Arewa ta tsakiya ya gaji Abdullahi Adamu.

Nadin Ministoci da Tinubu zai yi A game da zaben Ministoci, Lukman ya na ganin gwamnatin Bola Tinubu ba ta dauko irin mutanen da za su taimaka mata wajen cin ma manufofinta ba.

“Abu na uku shi ne yanayin wadanda ka ke ba aiki. Mai girma, a duk lokacin kamfen zaben 2023, daga cikin abin tallata ka shi ne ka iya nemo kwararru.

Idan aka duba yadda ya dauke ka fiye da makonni takwas kafin ka zabo Ministocinka, an yi tunanin ka na daukar lokaci ne domin zakulo fitattun kwararru.

Amma duba da wadanda ka zabo, ka ba mafi yawan jam’iyya da kuma ‘yan Najeriya kunya.

A zahiri yake ga duk masu tunani siyasa ya sha gaban komai. A halin yanzu, burin da ‘yan jam’iyya da ‘yan Najeriya ke da shi a gwamnatinka ya rushe”-Salihu Lukman.

El-Rufai

El-Rufai da kujerar Minista Ku na da labarin yadda rahoton DSS ya jawo sha’awar sake zama Minista ya fita daga ran Malam Nasir El-Rufai duk da an tantace shi a majalisar dattawa.

Dama tun can tsohon Gwamnan ya nuna rokon shi Bola Tinubu ya yi domin su yi aiki tare, daga baya aka ce binciken tsaro ya hana a tafi da Malam El-Rufai.

Osita Okechukwu ya na ganin kuskure ne Bola Ahmed Tinubu ya bar Nasir El-Rufai ya tafi a banza Idan tsohon Gwamnan ya zama minista, jagoran na APC ya na ganin APC za ta amfana a zaben 2027 Cif Okechukwu ya na da ra’ayin cewa El-Rufai ya cancanta ya kula da bangaren makamashi a Najeriya.

Tunibu ka ba mu kunya buɗaɗiyar wasiƙa daga shugaban APC
Tunibu ka ba mu kunya buɗaɗiyar wasiƙa daga shugaban APC

Osita Okechukwu

Osita Okechukwu wanda ya na cikin wadanda aka kafa jam’iyyar APC da su a Najeriya, ya yi kira da babbar murya ga Bola Ahmed Tinubu.

Osita Okechukwu ya gargadi Mai girma Bola Ahmed Tinubu cewa ka da ya cire Mallam Nasir El-Rufai a ministocinsa, Punch ta kawo rahoton.

An aika sunan Nasir El-Rufai zuwa majalisa, kuma har tsohon gwamnan ya bayyana a gaban Sanatoci, daga baya aka ji cewa ba a amince da shi ba.

Rashin El-Rufai babbar asara ce Da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja a ranar Lahadi, Darekta Janar na hukumar VON ya kuskure ne a ajiye tsohon Gwamnan Kaduna.

Okechukwu ya na da ra’ayin cewa El-Rufai zai bada gagarumar gudumuwa a gwamnati musamman idan ya samu mukami a bangaren wuta.

“Buhari ya yi asarar rasa El-Rufai, kuma babu wanda zai so kasarmu ko Shugaban kasa Tinubu ya rasa wannan ‘dan baiwa.

Jam’iyyarmu ta APC za ta amfana sosai da ministocin da su ka yi aiki a lokacin da mu ka dumfari babban zaben Najeriya a 2027.

Korar shi daga gwamnatin tarayya zai yi sanadiyyar fatattakar wasu karin ‘Yan Najeriya daga bangaren wutar lantarki.

Mutanen Najeriya da-dama su na kyale wutar gwamnati da ake fama da matsaloli yayin da talakawan kasar ke kukan tsada.

Mu na bukatar mutum na dabam kamar Nasir El-Rufai ya shawo kan matsalar lantarki.” – Osita Okechukwu.

Gaskiyar magana a kan El-Rufai Kamar yadda Daily Post ta rahoto, shugaban na VON ya ce bai cikin ‘yan kanzagin Nasir El-Rufai, kuma bai tunanin bai da tamka a gwamnatin Najeriya.

Illa iyaka ya na ganin tsohon Ministan na birnin Abuja ya fi sauran ire-irensa da-dama sanin yadda za a kawo gyara, musamman a bangaren makamashi.

Ya aka yi aka cire El-Rufai? Kun samu rahoton da ya nuna da kamar wahala Nasir El-Rufai, Abubakar Sani Danladi da Stella Okotete su iya zama Ministoci a gwamnati mai-ci.

Abin da ya faru da mabiyan El-Zakzaky sun taimaka wajen yakar tsohon Gwamnan Kaduna baya ga tulin korafi da kara a kotu da zargi da ke kan El-Rufai.

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Danna Nan: Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button