Tunibu Yace yazaɓo ministoci ne bisa cancanta
Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ministocin da aka rantsar a yau an zaɓo su ne bisa cancanta domin su taimaka wajen tafiyar da lamurran ƙasar.
Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi bayan rantsar da sabbin ministoci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
“Ƴan Najeriya na sa ran za ku yi aiki mai inganci kuma za ku sauke nauyin da aka ɗora muku.” – In ji Tinubu
Ya ƙara da cewa “Dole ne ku yi aikin da zai sanya ƴan Najeriya su sake amincewa da gwamnati.”
Tunibu
Ya bayyana cewa akwai babban nauyi a kan sabbin ministoci ganin irin manyan alƙawurran da gwamnatinsa ta ɗauka.
Shugaban ya kuma buƙaci sabbin ministocin da su yi aiki ba tare da nuna banbanci ba, inda ya ce: ”An ba ku wannan matsayi ne ba domin ɓangaren da kuka fito ku jihonhinku ba, sai dai domin ƙasa baki ɗaya.”
Illoli huɗu na rashin naɗa ministoci kan lokaci25 Yuli 2023
Najeriya
A watan Afrilu ne shugaban na Najeriya ya miƙa wa Majalisar Dattijan ƙasar sunayen mutum 45 domin tantantancewa a matsayin minsitoci.
Bayan haka nan shugaban na Najeriya ya bayyana ma’aikatun da kowane minista zai riƙe gabanin ranar ta yau da ake rantsarwar.
Sai dai ko a ranar Lahadi, shugaban ya fitar da wasu sauye-sauyen da ya yi na ma’aikatu ga wasu sabbin ministocin.
Table of Contents
Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?
Idan Kanada labarin da akeso a wallafa acikin wannan shafin namu mai albarka,zaka iya yimuna comments ta wajenda munka tanadarmuku.
Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki
Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.
Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page