Labarai

Unicef tace Juyin mulkin Nijar zai shafi yara sama da miliyan 2

Unicef tace Juyin mulkin Nijar zai shafi yara sama da miliyan 2

Unicef

Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce rikicin da Jamhuriyar Nijar ke ciki, tun bayan da aka hamɓarar da shugaban ƙasar a watan Yuli, zai shafi miliyoyin yara ƙanana.

Wata sanarwa da wakiliyar ta UNICEF a Nijar, Stefano Savi, ta fitar, ta ce halin da ake ciki a ƙasar abin damuwa ne da ke ƙara jefa ƴan ƙasar cikin halin ƙaƙaniƙayi da ya saka su buƙatar jin ƙai na gaggawa.

Wata sanarwa

Sanarwar ta ce rikicin zai shafi kimanin sama da yara miliyan biyu.

Nijar

Savi ta ce akwai matukar damuwa ganin yadda ake ci gaba da fuskanatar ƙarancin wutar lantarki a ƙasar, wadda da ita ne ake amfani wajen ajiye alluran rigakafi na yara.

Haka kuma ta sake nanata damuwar da ake da ita kan yadda har wasu kwantenoninta 21 da ke ɗauke da kayan ceton rai suka maƙale a kan iyakar Nijar da Benin, sannan akwai wasu 29 da za a shigo da su Nijar da ke kan teku ɗauke da abincin gaggawa da sirinji.

Ecowas

“Muna kira ga Nijar da ECOWAS da su tabbatar da rikicin da suke da juna bai haifar da cikas ba ga ayyukan jin ƙai ga iyalai da yara ƙanana da ke buƙatar kulawa ta gaggawa,” in ji Savi.

Ta buƙaci a bai wa shirye-shiryen jin ƙai da ake gudanar da su a Nijar ɗin kariya daga dukkan wani takunkumi.

UNICEF ta ce tun ma kafin samun rikici a Nijar, akwai kusan yara miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar da ke da shekaru ƙasa da biyar da aka yi kiyasin suna fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.

Jamhuriyar Nijar da ke yankin sahel na cikin ƙasashen duniya da ke fama da tarin matsaloli da kuma talauci.

Unicef tace Juyin mulkin Nijar zai shafi yara sama da miliyan 2
Unicef tace Juyin mulkin Nijar zai shafi yara sama da miliyan 2

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Idan Kanada labarin da akeso a wallafa acikin wannan shafin namu mai albarka,zaka iya yimuna comments ta wajenda munka tanadarmuku.

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button