Labarai

Waƙilan Ecowas sun koma Nijar don tattaunawa da sojojin mulki 2023

Waƙilan Ecowas sun koma Nijar don tattaunawa da sojojin mulki 2023

Waƙilan Ecowas.

Tawagar ƙarƙashin jagorancin Abdulsalami Abubakar (hagu) ta samu tarba daga Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine

Kwamitin shiga tsakani.

Kwamitin shiga tsakani na Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (Ecowas) ya isa Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin ganin an shawo kan dambarwar siyasar ƙasar ta hanyar lumana.

Tawagar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ta samu tarba daga Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, wanda sojoji suka naɗa.

Ana sa ran za su tattauna da jagoran mulkin soja, Janar Abdourahmane Tchiani, game da yadda za a mayar da mulki ga farar hula.

Ecowas.

Ecowas na son sojojin su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki, wanda suke tsare da shi tun 25 ga watan Yuli.

Waƙilan Ecowas sun koma Nijar don tattaunawa da sojojin mulki 2023
Waƙilan Ecowas sun koma Nijar don tattaunawa da sojojin mulki 2023

Juyin mulki.

Juyin mulkin da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka yi wa Bazoum ranar 26 ga watan Yuli, ya janyo zazzafan mataki daga Ecowas.

Komawar kwamatin na zuwa ne kwana ɗaya bayan Ecowas ta ce taron manyan hafsoshinta na kwana biyu a birnin Accra ya saka ranar kai yaƙi Nijar.

Kwamishinan harkokin siyasa na Ecowas, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya ambato su, suna cewa: “Mun shirya shiga a duk lokacin da aka ba mu umarni”.

Amma dai, Ecowas ta jaddada cewa duk da wancan mataki ƙofofin sulhunta rikici ta hanyar diflomasiyya za su ci gaba da kasancewa a buɗe.

A baya, wa’adin Ecowas da ƙoƙarin diflomasiyya ba su iya tanƙwara sojoji masu mulki a Nijar ba wajen mayar da hamɓararren Shugaba Bazoum kan karagar mulki.

Wata majiya a cikin kwamitin diflomasiyyar na Ecowas, ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ta ce saɓanin ziyarar farko, a wannan karo suna sa ran samun kyakkyawar tarba daga shugabannin mulkin sojan Nijar.

A karon farko, rahotanni sun ce kwamitin Abdulsalami Abubakar bai samu kyakkyawar tarba a Yamai ba, hasali ma jami’an diflomasiyyar ba su iya shiga gari ba, daga filin jirgin saman Diori Hamani.

Babu masaniya a kan irin tuntuɓa ta bayan fage da aka ci gaba da yi kan rikicin siyasar na Nijar kafin wannan lokaci, amma majiya daga kwamitin ta ce suna da ƙwarin gwiwa a wannan karo za su gana da Janar Abdourahamane Tchiani.

Ta ce: “Duk da yake Ecowas ta cimma waccan matsaya a birnin Accra, amma har yanzu babu wanda yake son yin yaƙi.”

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button