Labarai

Ƴan ta’adda sun yi garkuwa da masu bautar 8 ƙasa a Najeriya

Ƴan ta’adda sun yi garkuwa da masu bautar ƙasa 8 a Najeriya

Zamfara

Bayanai daga jihar Zamfara ta Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan bautar kasa 8, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Sokoto inda aka tura su don yin aikin bautar kasa.

Tun farko daliban su 11 sun shiga motar haya mallakin gwamnatin jihar Akwa Ibom da nufin zuwa jihar Sokoto, inda aka tura su don aikin bautar-kasar, sai dai fitar su daga birnin Gusau ke da wuya ‘yan bindigar suka far musu.

Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa uku daga cikinsu sun yi nasarar tserewa, sai dai ‘yan bindigar sun shiga da guda 8 da kuma direban motar cikin daji.

Wani jami’i daga kamfanin motocin hayar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ba zato ba tsammani suka ga ƴan bindigar a tsakiyar titi, abin da ya tilasta wa direban motar taka burki, nan take kuma suka buƙaci su fito daga motar sannan suka kada daliban da direban motar cikin daji, bayan da saura suka tsere.

Guda daga cikin iyalan daliban ya shaida wa manema labarai cewa tuni ƴan bindigar suka tuntuɓe su tare da buƙatar su kai naira miliyan 4 kan kowanne dalibi a matsayin kuɗin fansa.

Hausaone

Hausaone ta yi iya bakin koƙarinta wajen jin ta bakin jami’an tsaro da bangaren gwamnatin jihar Zamfara don neman ƙarin bayani, amma hakan ya ci-tura, inda kakakin ƴan sandan jihar Yazid Abubakar ya gaza bayar da  bayani duk da kiran da muka riƙa yi masa da kuma alkwarin ba mu cikakken bayani.

Shi kuma mataimakin gwamna kan harkokin yada labarai Mustapha Jafaru Kaura bai ɗauki waya ba bayan mun kira shi.

Table of Contents

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan matsala da tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Ƴan ta'adda sun yi garkuwa da masu bautar 8 ƙasa a Najeriya
Ƴan ta’adda sun yi garkuwa da masu bautar 8 ƙasa a Najeriya

Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button