Labarai

Yanda ake sukar tinubu akan yunƙurin tura sojoji Nijar

Yanda ake sukar tinubu akan yunƙurin tura sojoji Nijar

Sukar da Tinubu ke sha kan yunƙurin tura sojoji Nijar

Shugaban Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu na shan suka a gida game da barazanar da ya yi ta amfani da ƙarfin soja don kawo ƙarshen juyin mulkin da sojoji suka yi a maƙwabciyarsu Nijar.

‘Yan majalisar ƙasar sun tafka muhawara a kan batun ranar Asabar, inda suka ƙi goyon bayan matakin duk da cewa jam’iyyar APC ce mai mulki ke jagorancin majalisar.

Yanda ake sukar tinubu akan yunƙurin tura sojoji Nijar

Lamarin ya fi ƙamari musamman ga ‘yan majalisar da suka fito daga jihohin da ke da iyaka da Nijar mai tsawon kilomita 1,500, haka nan kuma ‘yan ƙasa da dama sun yi tir da yunƙurin.

Ƙungiyar Ecowas

Ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma ce ta saka wa’adin ranar Lahadi da ta wuce ga sojojin da su sauka daga mulki ko kuma su fuskanci ƙarfin soja.

Ana kallon matakin a matsayin na Tinubu kaɗai saboda shi ne shugaban Ecowas, kuma Najeriya ce babbar mamba a cikinta.

Duk da cewa sojojin sun yi buris da wa’adin, Ecowas ba ta mayar da martani ba ta hanyar tura dakaru. Hakan ya kwantar da hankalin ‘yan Najeriya da dama, waɗanda suka fi son a bi hanyoyin difilomasiyya.

Da ma can wasu na ganin wa’adin kamar ba mai yiwuwa ba ne ganin cewa sai Najeriya da sauran ƙasashen Ecowas sun nemi amincewar majalisunsu kafin tura dakarun Nijar.

Kazalika, wasu sun yi mamakin yadda Najeriya ta katse wa Nijar wutar lantarki bisa umarnin Shugaba Tinubu, inda aka jefa babban birnin Yamai da wasu jihohi cikin duhu.

Masu sukar gwamnati na cewa hakan ya saɓa da yarjejeniyar da aka ƙulla wadda ta bai wa Najeriya damar gina madatsar ruwa a Kogin Neja, duk da cewa magoya bayan Tinubu kan ce an ɗauki matakin ne saboda a matsa wa sojoji su sauka daga mulki.

Najeriya da Nijar na da alaƙa mai ƙarfi ta fuskar tattalin arziki da al’adu, kuma duk wani yaƙi da za a kai wa Nijar zai shafi arewacin Najeriya, yankin da da ma tuni yake fama da matsalolin tsaro.

Wasu ƙungiyoyi na addini da fitattun ‘yan Najeriya da dama sun gargaɗi Tinubu game da “gaggawa wajen shiga rikici da maƙwabta saboda siyasar duniya”.

“Wajibi ne mu kare dimokuraɗiyya. Babu shugabanci ko ‘yanci ko doka da oda idan babu dimokuraɗiyya.

Ba za mu yarda da juyin mulki akai-akai ba a Afirka ta Yamma,” in ji Tinubu jim kaɗan bayan ya zama shugaban Ecowas.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa shugaban ƙasa bai isa ya tura sojoji zuwa wata ƙasa ba ba tare da amincewar majalisa ba – ma’ana majalisar dokoki da ta dattijai.

Farfesa Khalifa Dikwa

“Ecowas ta yi ɓarin zance, shugaban Najeriya ma ya yi ɓarin zance,” a cewar Farfesa Khalifa Dikwa, malami a Jami’ar Maiduguri kuma mamba a ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya.

Cikin wani sanarwa da suka fitar bayan tattaunawar sirri, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya nemi Ecowas ta ci gaba da “lalubo hanyoyin sasanta rikicin cikin gaggawa”.

Babu mamaki aƙidar Tinubu ta yaƙi da juyin mulki na da alaƙa d abin da ya faru da shi. Bai wuce shekara ɗaya ba a matsayin ɗan majalisa a 1990 lokacin da aka soke zaɓukan, aka rusa majalisar sannan Janar Sani Abacha ya ƙwace mulki.

Ya shiga ƙungiyoyin fafutikar dawo da mulkin farar hula, abin da ya haɗa shi rigima da sojoji har suka sa ya tafi gudun hijira.

Ya koma Najeriya a 1998 bayan mutuwar Sani Abacha, ɗaya daga cikin shugabannin Najeriya mafiya rashin imani.

Sai dai wasu ‘yan Najeriya da dama na ganin Ecowas ta yi gaggawar ba da wa’adi ga sojojin Nijar ɗin, kuma Shugaba Tinubu bai yi tunanin da yawa ba game da tasirin da yaƙin zai yi idan aka yi amfani da ƙarfi.

“Nijar ɓangare ne na arewacin Najeriya har zuwa lokacin da aka yi Taron Berlin [na 1884 zuwa 1885 lokacin da ƙasashen Yamma suka tsaga iyakokin ƙasashen Afirka]. Kana tunanin Arewa za ta yaƙi kanta da kanta ne?” in ji Farfesa Dikwa

Saɓanin wanda ya gada Muhammadu Buhari, Shugaba Tinubu ba shi da masaniya kan harkokin soja, haka ma mai ba shi shawara kan tsaro, Nuhu Robadu, wanda ɗan siyasa ne.

Yanda ake sukar tinubu akan yunƙurin tura sojoji Nijar
Yanda ake sukar tinubu akan yunƙurin tura sojoji Nijar

Hafsoshin tsaro na Ecowas sun ce ƙarfin soja “shi ne mataki na ƙarshe” da za su ɗauka bayan zaman da suka yi a makon da ya gabata.

Duk da cewa wasu ƙasashen Afirka ta Yamma sun yi alƙawarin shiga yaƙin, abu ne mawuyaci su iya yin hakan ba tare da Najeriya ba, idan majalisa ba ta amince da buƙatar Tinubu ba.

Tinubu na sanye da hula biyu ne – ta Ecowas da kuma ta shugabancin Najeriya. Ɗaya ta sharɗanta ɗaukar matakai don kare dimokuraɗiyya da kuma Afirka ta Yamma, amma za ta iya jawo abubuwa marasa daɗi ga ɗayar

Za'a karawa fetur kudi saboda tashin dala a Najeriya
Yanda ake sukar tinubu akan yunƙurin tura sojoji Nijar

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Danna Nan: Barcelona na son Bernado Silva 2023

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button