Labarai

Za’a karawa fetur kudi saboda tashin dala a Najeriya

Za’a karawa fetur kudi saboda tashin dala a Najeriya

Acikin shirin namu nayau zakuji cewa, feturke siyarwa a naira 617 a yanzu zai ƙara tashi.

Dalilin da ya sanya kungiyar manyan dillalan man fetur na kasa wato IPMAN ta mayar da martani kan wannan jita-jita.

Chinedu Okoronkwo

Chinedu Okoronkwo shi ne shugaban ƙungiyar na ƙasa ya ce “matuƙar dala za ta tashi farashin man fetur zai tashi shi ma”.

Dalili

“Ba ma iya samun dala a bankunan kasuwanci kuma idan kaje kasuwar bayan fage farashin ya wuce duk yadda kake zato,” in ji Chinedu.

zantawa da shugaba

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Bashir Dan Mallam, ya shaida wa hausaone cewa “a yanzu farashin mai ya tashi a Legas da wurare da yawa, yanzu fa masu gidajen mai sai dai su haɗa hannu su sayi mota guda”.

Masu Gidajen mai

“Ta yaya za mu iya tunkarar mutanen Najeriya da wannan tsada, ina ganin sai dai mu rufe gidanjen man, mu zuba wa sarautar Allah ido,” in Bashir Danmalan.

Yanda ake sayen maiƙasart

Man da ake saya daga waje zuwa Najeriya ana sayansa ne da dalar Amurka, wadda farashinta ya haura naira 940 a cewar wani ɗan kasuwa da ke Legas a Najeriyar.

Za'a karawa fetur kudi saboda tashin dala a Najeriya
Za’a karawa fetur kudi saboda tashin dala a Najeriya

Tashinta kuma zai iya haifar da tashin farashin mai wanda shi kuma ake sayar da shi a naira 617, kuma ba a san ko nawa zai iya komawa ba idan ƙarin da ake tsammani ya auku.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed TInubu ne dai ya sanar da cire farashin mai a ƙasar, a ranar da aka rantsar da shi a matsayin shugaba.

Kuma tun bayan nan farashin abubuwa ke ƙara ta’azzara a ƙasart

Amma Mizakuce dangane da wannan lamarin?

Danna Nan: Barcelona na son Bernado Silva 2023

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button